Jiga-jigan da suka yi nasara da wadanda suka sha kasa yayin da APC ta nada shugabanni
- Rahotanni su na zuwa cewa bangarorin APC da suke tare da Ministoci da Sanatoci za su sha kasa a tafiyar jam’iyya
- An yi babu ‘Yan taware inda wadanda suke tare da Gwamnoni su ka yi nasara da aka rantsar da shugabannin jihohi
- Irinsu Adamu Adamu, Omo-Agege, Oyetola sun yi galaba, tsagin su Keyamo, Tuggar, Aregbesola sun sha kashi
Abuja - A yau Alhamis, 2 ga watan Fubrairu 2022 ake rantsar da shugabannin APC na reshen jihohi. Punch ta ce wadanda ke tare da gwamnoni sun yi galaba.
Wasu daga cikin kusoshin jam’iyyar APC mai mulki da suka rasa ikon jam’iyya a hannun gwamnonin jihohinsu sun hada da wasu Ministoci na tarayya.
Daga cikin Ministocin akwai Rauf Aregbesola, Festus Keyamo SAN da kuma Alhaji Lai Mohammed.
Tsofaffin gwamnoni kamar su Ibikunle Amosun da Abdulaziz Yari da kuma su Sanata Kabiru Marafa sun gaza karbe jam’iyya daga hannun abokan fadansu.
Har zuwa dazu a jihohi irinsu Osun, shugaban ‘yan taware na APC, Alhaji Rasaq Salinsile ya ce babu tabbacin wani bangare na shugabannin za a rantsar a yau.
Shugaban APC na Osun, Prince Gboyega Famoodun wanda yake tare da gwamnatin Gboyega Oyetola ya ce babu tababa a kan cewa su za su rike jam’iyyar APC.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A jihar Kwara, shugabannin ‘yan taware na APC ba su san da bikin rantsar da shugabannin jihohi ba. Amma kuma an gayyaci mutanen Prince Sunday Fagbemi.
Bayan Kwara da Osun, a Ogun ma da alamun cewa sakatariyar APC za ta rantsar da bangaren Yemi Sanusi ne, tayi watsi da ‘yan tawaren da ke tare da Amosun.
'Yan siyasan Zamfara sun sha kashi
Rahoton ya ce a Zamfara an yi fatali da 'yan tsagin Kabiru Marafa da na Abdul’Aziz Yari yayin da uwar jam’iyya ta tafi da mutanen da ke tare da gwamna Matawalle.
Rikicin gidan APC tsakanin Ovie Omo-Agege da Keyamo ya ki karewa a Delta, inda aka zabi a rantsar da Omens Sobotie a matsayin shugaban jam’iyya na jiha.
A Bauchi, mutanen Adamu Adamu za a rantsar, hakan ya na nufin babu labarinsu Yusuf Tugar. Kawo yanzu babu labarin wanda aka zaba tsakanin tsagogin Kano.
Inda ake ta rikici
Jihohin da ake samun sabani tsakanin Gwamnoni da su manyan jam’iyya sun kunshi: Osun, Ogun, Kwara, Kebbi, Kano, Delta, A/Ibom, Rivers, Bauchi da Zamfara.
Ku na da labari cewa tsohon ‘dan majalisar Kaura Namoda/Birnin Magaji, Aminu Sani Jaji ya caccaki Alhaji Abdulaziz Yari, ya ce ba a san da zamansa a jam'iyya ba.
Asali: Legit.ng