2023: Kungiya ta huro wuta, ta na so a ba matashi kujerar Mataimakin shugaban kasa

2023: Kungiya ta huro wuta, ta na so a ba matashi kujerar Mataimakin shugaban kasa

  • Dole a rika ware kujeru saboda matasa a cewar kungiyar matasa ta Youth Engagement and Inclusion Agenda
  • Wannan kungiya ta bukaci a rika damawa da matasa a siyasar Najeriya domin masu tasowa su fara shiryawa
  • Shugaban Youth Engagement and Inclusion Agenda, Idris Aregbe yace su na son mataimakin shugaban kasa

Lagos - An samu wata kungiya mai suna Youth Engagement and Inclusion Agenda da take so a warewa matasa kujerar mataimakin shugaban kasa.

Punch ta ce Youth Engagement and Inclusion Agenda tana so a rika yi da matasa a kasar nan.

Da yake jawabi a garin Ikeja, jihar Legas, shugaban wannan kungiya na kasa watau Idris Aregbe ya ce duk wata jam’iyya ta ba matashi takara a zaben 2023.

Aregbe yana so ya zama an ba matashi mai jini a jikinsa takarar mataimakin shugaban kasa a zabe mai zuwa a dukkanin jam’iyyun siyasa da ake da su.

Kara karanta wannan

Kwankwaso, GEJ, Osinbajo, Atiku: ‘Yan siyasan da har yau ba su ce komai kan 2023 ba

Haka zalika a wajen wannan taro wanda shi ne na farko da kungiyar tayi a tarihinta, Idris Aregbe ya ce duk masu neman zama gwamna su tafi da matasa.

Kungiyar ta na so ‘yan takarar gwamna su zakulo matasa da suka cancanta domin su yi masu takarar mataimakin gwamna a zaben da za ayi a shekarar badi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

APC Lagos
Wasu Magoya baya a zaben 2019 Hoto: @jidesanwoolu
Source: Twitter

Ina fa'idar tafiya da matasa?

A ganin Youth Engagement & Inclusion Agenda, yin hakan zai taimaka wajen samar da wadanda za su shugabanci Najeriya idan manyan sun bar mulki.

“Bukatarmu bamai wahala ba ce ga duk wani ‘dan takarar shugaban kasa, domin wannan zai hana a samu gibi a lokacin da shugabannin da ake da su a yau suka yi ritaya daga siyasa, kuma ana bukatar a kawo mafita ga matsalolin da aka samu kai.”
“Ware wadannan kujeru ga matasa shi ne hanyar da ta fi wajen koyawa matasa yadda za su koyi shugabanci daga jagororin da sun goge a wannan harka.”

Vanguard ta rahoto Mista Aregbe yana mai cewa ba su tare da wata jam’iyya, burinsu kurum shi ne su ga ‘danuwansu ya dare kujerar mataimakin shugaban Najeriya.

Kara karanta wannan

Sabon lale: Atiku ya jefar da abokin takararsa, zai zabi Gwamnan PDP ya yi masa mataimaki

Kungiyar ta ce ta duba matsayar matasan Najeriya bayan zabe, ta ga cewa ya kamata ayi gyara.

Wa za a zaba a 2023?

Jigon jam'iyyar hamayya ta PDP a Arewacin Najeriya, Sule Lamiɗo,ya yi fatali da batun tsarin mulkin karba-karba wajen tsaida ɗan takarar shugaban kasa a Najeriya.

Tsohon gwamnan jihar Jigawa ya ce Najeriya na bukatar nagartaccen jagora wanda jam'a suke kauna, ya na sukar masu nacewa a kan sai an kai mulki zuwa wani yanki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng