2023: Tsohon ‘Dan Majalisar Kano ya hango Tinubu a Aso Villa, ya ba ‘Yan adawa shawara

2023: Tsohon ‘Dan Majalisar Kano ya hango Tinubu a Aso Villa, ya ba ‘Yan adawa shawara

  • Abdulmumin Jibrin ya na ganin Asiwaju Bola Tinubu zai tsallake duk wasu shinge, ya samu takara
  • Tsohon ‘dan majalisar tarayyar ya ce jigon na APC ya fi kowa samun dama mai kyau na lashe zabe
  • Hon. Jibrin ya yi kira ga masu sukar Tinubu, su yi amfani da karfinsu wajen saida na su ‘dan takarar

Abuja - Honarabul Abdulmumin Jibrin daya daga cikin wadanda suka fito suka nuna goyon-baya ga Bola Tinubu, ya ce gwaninsu ne zai lashe zaben 2023.

Hon. Abdulmumin Jibrin wanda shi shugaban kungiyar magoya baya ta Tinubu Support Management Council yana ganin Bola Tinubu ya ci zabe.

Da yake magana a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, 31 ga watan Junairu 2022, Jibrin ya ce Tinubu ya dace da takara, kuma ya fi kowa damar cin zabe.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kusa kwamushe Malamin Addini saboda hangen faduwar Tinubu a 2023, ya yi martani

“A 2015, shugaba Muhammadu Buhari ya sha gaban sauran masu neman shugaban kasa. Aka tsaida shi takara, sai kuma ya yi nasara.”
“A tseren zaben 2023, Bola Ahmed Tinubu ne a kan gaba, ya cancanci ya yi takara, ya dace, kuma shi ne ya fi kowa damar lashe zaben.”
“Shi zai zama ‘dan takarar jam’iyyar APC. Zai yi galaba a zaben shugaban kasa, kuma zai yi aikin da ya kamata, da yardar Ubangiji.”

- Abdulmumin Jibrin

Tinubu a Aso Villa
Jirbin yana tare da Bola Tinubu
Asali: UGC

Can kuma an ji tsohon ‘dan majalisar na Kiru da Bebeji yana mai cewa Bola Tinubu zai yi nasara a zaben fitar da gwani da babban zabe na kasa idan Allah ya so.

Jibrin ya ce ko ta ya aka bullowa zaben fitar da 'dan takara a APC, Tinubu ne zai samu tuta.

Kara karanta wannan

Wuyan Abokin takarar Atiku a zaben 2019 ya yi kauri, zai nemi Shugaban kasa a 2023

“Ko ‘yar tinke aka yi ko ma dai ‘ya ‘yan jam’iyya suka yi zabe, Tinubu zai lashe zaben tsaida ‘dan takara da babban zabe idan Allah ya so.”
“A maimakon ka bata lokaci da karfinka wajen yawan suka, ka maida hankali wajen saida mai neman shugaban kasa da ‘dan takararka.”

- Abdulmumin Jibrin

Kungiya ta na so Amaechi ya karbi mulki a 2023

Wata kungiyar matasan Arewa mai son kawo gyara watau Coalition of Northern Youth for Good Governance ta ce mulkin Najeriya a 2023 sai irinsu Rotimi Amaechi.

Shugaban CNYGG, Bilal Dakiyak ya ce Amaechi bai tsufa ba, ya san kan-aiki, kuma Muhammadu Buhari ya kawo shi, don haka ya san duk mafitar matsalolin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng