Wuyan Abokin takarar Atiku a zaben 2019 ya yi kauri, zai nemi Shugaban kasa a 2023

Wuyan Abokin takarar Atiku a zaben 2019 ya yi kauri, zai nemi Shugaban kasa a 2023

  • Watakila tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi zai fito neman tikitin jam’iyyar PDP a zaben 2023
  • Obi ya ce muddin PDP ta tsara cewa ‘dan takarar shugaban kasa zai fito daga Kudu, da shi za a gwabza
  • A 2019, Obi ne ya zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP tare da Atiku Abubakar

Nigeria - Idan har jam’iyyar PDP ta kai takarar shugaban kasa zuwa bangaren kudancin Najeriya a zaben 2023, tsohon gwamna Peter Obi zai nemi takara.

Peter Obi wanda ya yi takara tare da Atiku Abubakar a zaben da ya wuce, ya nuna cewa zai iya fitowa neman shugabancin Najeriya a zaben 2023 da za ayi.

Obi ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a safiyar Talatar nan, 1 ga watan Fubrairu 2022.

Kara karanta wannan

Sabon lale: Atiku ya jefar da abokin takararsa, zai zabi Gwamnan PDP ya yi masa mataimaki

“Kwarai, zan shiga filin daga in nemi damar yi wa wannan kasarnan ta mu hidima idan jam’iyyarmu ta PDP ta kai takara zuwa yankin kudu.”
“Idan kuma an bar kofar neman takarar a bude ga kowane yanki, haka nan ma ‘yan Najeriyan za su ji daga gare ni.”

- Peter Obi

Zaben 2023 ya gabato

Jaridar The Cable ta ce sanarwar da Peter Obi ya bada ta zo ne jim kadan bayan gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya ce zai tsaya takara.

Peter Obi
Peter Obi ya na kamfe a 2019 Hoto: thewhistler.ng
Asali: UGC

A 2020 ne tsohon gwamnan na Anambra ya fito shafinsa na Twitter har wa yau, ya nemi ayi watsi da fastocin takararsa da aka gani tare da Rabiu Kwankwaso.

A wancan lokaci an yi tunanin cewa ‘dan siyasar bai da niyyar neman shugabancin Najeriya a 2023.

Kara karanta wannan

2023: Mai neman kujerar shugaban kasa a PDP, ya dawo gida zai yi takarar Gwamnan Jiha

Wanene Peter Obi

Mista Peter Obi babban ‘dan kasuwa ne a Najeriya wanda ya shiga siyasa, kuma ya yi nasarar zama gwamna a jihar Anambra a jam’iyyar APGA a 2006.

Kafin a je ko ina sai kotu ta sauke Obi daga gwamna. A 2007 ya dawo kan mukaminsa, har ya zarce a mulki, a 2014 wa’adinsa na shekaru takwas ya cika.

A Oktoban 2014 ne aka ji cewa tsohon gwamnan ya fice daga jam'iyyar APGA, ya shiga PDP.

Atiku ya rabu da Obi?

Ku na sane cewa rade-radin da yake yawo shine Atiku Abubakar ya saduda, zai yi watsi da Peter Obi ya rungumi Nyesom Wike su yi takara tare a zaben da za ayi a 2023.

Ana zargin Obi da kin kashe kudinsa a zaben 2019, sannan bai iya tsinanawa Atiku da jam’iyyar PDP komai ko a jihar da ya fito ba, hakan ta sake ganin bai da jama'a.

Kara karanta wannan

2023: Jerin abubuwa 6 da za su tare hanyar Atiku Abubakar ya zama Shugaban Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng