Sabon lale: Atiku ya jefar da abokin takararsa, zai zabi Gwamnan PDP ya yi masa mataimaki

Sabon lale: Atiku ya jefar da abokin takararsa, zai zabi Gwamnan PDP ya yi masa mataimaki

  • Ana jita-jitar Atiku Abubakar zai yi takara da Gwamna Nyesom Wike a matsayin mataimakinsa
  • Babu mamaki ‘dan siyasar zai yi watsi da Peter Obi idan ya samu tikitin PDP a zabe mai zuwa na 2023
  • Hakan ya fara raba kan ‘Yan PDP, musamman masu so a ba yankin Kudu maso gabas takarar shugaban kasa

Alamu su na nuna cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar zai dauki gwamna Nyesom Wike a matsayin abokin takararsa a zaben 2023.

Jaridar Business Day ta ce Alhaji Atiku Abubakar wanda yana cikin masu neman kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa, ya yi watsi da Peter Obi.

A zaben 2019, Peter Obi ne ya tsayawa Atiku a matsayin ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa, wanda hakan ya fusata manyan PDP daga yankin Kudu.

Kara karanta wannan

2023: Jerin abubuwa 6 da za su tare hanyar Atiku Abubakar ya zama Shugaban Najeriya

Wannan karo ana rade-radin cewa ‘dan siyasar zai ajiye tsohon gwamnan na jihar Anambra, ya tafi da gwamnan jihar Ribas mai-ci watau Nyesom Wike.

Inda Obi ya samu cikas

Rahoton ya nuna cewa ana ganin tsohon gwamnan ya lakanci tattalin arziki amma kuma bai taimaka da dukiyarsa wajen ganin sun yi nasara a 2019 ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Atiku ya na kamfe
Atiku Abubakar da Peter Obi Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

Haka zalika Obi bai iya kawowa tikitinsu kuri’un kirki ba. Asali ma dai tsohon gwamnan ya gagara lashe jiharsa ta Anambra da yankin kudu maso gabas.

Wata majiya ta ce Obi bai da karfi a siyasa a wajen shiyyar da ya fito. Mutane su na kaunarsa ne kurum saboda ya kware a tattali, wanda cin zabe ya wuce haka.

Na-kusa da Atiku sun fahimci tun da Obi ya sauka daga gwamna ya shiga PDP, bai taba daura wanda yake so a matsayin ‘dan takarar gwamna a Anambra ba.

Kara karanta wannan

Na sanar da Atiku cewa ya tsufa kuma gajiye ya ke, ba zai iya shugabanci ba, Gwamnan Bauchi

Ba a iya dogon Turanci ba ne

“Duk da ya iya Ingilishi mai kyau, ya fahimci tattalin arziki, lashe zabe ya wuce wannan. Me ya iya kawowa a zabe”?
“Idan za ka yi nasara a zabe ka na bukatar kudi, mutane, da kafuwa da kyau a siyasa, za ka samu Wike da wannan.”
“Nyesom Wike zai yi kyau da abokin takara, ba za ka yi watsi da shi, musamman idan ka so ka ci zabe a Najeriya a yau.”

- Wata majiya kusa da Atiku

Ina APC za ta sa kanta?

Rahoto ya zo cewa ‘Yan siyasan Kudu da Arewa su na neman mulkin Najeriya a APC, shugabanninta sun samu kansu a tsakiyar tsilla-tsilla gabanin 2023.

Duk da yankin Arewa ake shirin kai kujerar shugabancin jam’iyya na kasa, ba abin mamaki ba ne idan aka ga 'dan takarar shugaban kasa ya sake fitowa daga Arewa.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: PDP ta shiga matsi, gwamnonin kudu 3 sun ce ba ruwansu da takarar Atiku

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng