Baki ya ke yanka wuya: An bukaci Tinubu ya bada hakurin abubuwan da ya fada tun a 1997

Baki ya ke yanka wuya: An bukaci Tinubu ya bada hakurin abubuwan da ya fada tun a 1997

  • Wasu ‘ya ‘ya da shugabannin jam’iyyar APC a yankin Arewa sun yi kira ga Asiwaju Bola Tinubu
  • Kungiyar ta APC ta bukaci Bola Tinubu ya lashe amansa kan wasu kalaman da ya yi a shekarar 1997
  • Jagoran na APC mai neman shugabanci a 2003 ya taba cewa shi bai yarda Najeriya kasa daya ce ba

Daily Trust ta ce ‘ya ‘yan jam’iyyar na APC mai mulki su na so Bola Tinubu ya janye wasu kalamai da ya yi a shekarun baya kafin ya san zai nemi shugabanci.

Tun da yanzu ya na da niyyar neman takarar shugaban kasa, magoya bayan na APC sun nemi Tinubu ya janye kalaman da ya yi kan rashin imani da Najeriya.

Kara karanta wannan

Zaben APC: ‘Yan Jam’iyya a Arewa sun tsaida ‘Dan amanar Buhari a matsayin ‘dan takararsu

Shugaban kungiyar ta magoya-bayan APC, Saleh Mandung Zazzaga, ya shaidawa ‘yan jarida cewa idan Bola Tinubu bai lashe amansa ba, zai iya gamuwa da cikas.

Da yake zantawa da ‘yan jarida a garin Jos, jihar Filato, Saleh Mandung Zazzaga ya ce kalaman na Tinubu za su iya jefa shi da jam’iyyarsu duk a cikin matsala.

Jawabin Saleh Mandung Zazzaga

“A wata hira da aka yi da Bola Tinubu wanda ta fito a ranar 13 ga watan Afrilu, 1997, an rahoto shi yana cewa ‘ban yarda Najeriya kasa-daya ba’.”
“Tun da an fito da wannan tattaunawa saboda ya bayyana niyyar neman takarar shugaban kasa, mutane sun fara jefa tambayoyi masu hadari.”
Tinubu
Asiwaju Bola Tinubu Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

“Mutane su na ta yi mani dariya (APC), su na cewa ‘Idan Tinubu bai yarda Najeriya kasa daya ce ba, to ya aka yi yake neman shugabancinta?’ - Saleh Mandung Zazzaga

Kara karanta wannan

Takarar shugaban kasa a 2023: Babatu 3 da Tinubu ya yi da ka iya sa ya fadi a 2023

Ya kamata Tinubu ya wanke kansa

A cewar Saleh Mandung Zazzaga, abin da Tinubu ya fada a wancan lokaci ya na ta yawo har a zuciyar ‘yan jam’iyyarsu ta APC, hankalinsu bai kwanta ba.

Zazzaga ya ce a matsayinsa na jagora a jam’iyya a matakin kasa, ya kamata Tinubu ya ce wani abu.

“Abin da ya fi kamata Bola Tinubu ya yi shi ne, ya fito ya nemi afuwar ‘Yan Najeriya a kan wannan kalamai da ya yi kafin a dawo mulkin farar hula a shekarar 1999.”
“Kuma ya bayyana abin da ya sa ya yi wannan magana, ya fadi ko hakan yake nufi ko ba hakan ba. Akalla wannan zai kwantar da hankalin masu masa wani kallo.”

- Saleh Mandung Zazzaga

Jonathan zai dawo APC?

Ku na da labari cewa wasu jiga-jigan jam’iyyar APC a Arewacin Najeriya sun kitsa yadda za a sa Goodluck Jonathan ya sauya sheka daga PDP, ya yi takara a APC.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tinubu ya dura Neja, ya shiga ganawa da IBB kan batun takara a 2023

Nufinsu na tsaida tsohon shugaban Najeriyar takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ya gamu da tasgaro bayan an yi la’akari da wasu abubuwa a game da zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng