Zaben APC: ‘Yan Jam’iyya a Arewa sun tsaida ‘Dan amanar Buhari a matsayin ‘dan takararsu

Zaben APC: ‘Yan Jam’iyya a Arewa sun tsaida ‘Dan amanar Buhari a matsayin ‘dan takararsu

  • Kusoshin APC daga Arewa maso tsakiya sun yi taro a kan zaben shugabannin jam’iyya da za ayi
  • Kan ‘ya ‘yan jam’iyyar sun hadu a kan cewa Saliu Mustapha ya fi kowa cancancta da ya rike APC
  • Mallam Mustapha shi ne mai mafi karancin shekaru cikin masu neman shugabancin jam’iyyar na kasa

Kwara - Wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC a Arewa maso tsakiyar Najeriya, sun tsaida Saliu Mustapha a matsayin ‘dan takararsu a zaben da za ayi.

Daily Trust ta ce jagororin na APC mai mulki da suka fito daga shiyyar Arewa ta tsakiya sun zabi Mallam Saliu Mustapha ya zama wanda suka yi wa mubaya’a.

Malam Saliu Mustapha ya na cikin masu neman takarar kujerar shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar CPC da ta narke a cikin APC shi ne mai mafi karancin shekaru a ‘yan takarar, yanzu haka shekarunsa 49 a Duniya.

Kara karanta wannan

Baki ya ke yanka wuya: An bukaci Tinubu ya bada hakurin abubuwan da ya fada tun 1997

Tun ba yau ba Mustapha yake tare da shugaba Muhammadu Buhari, da shi aka yi tafiyar ANPP a baya, sannan yana cikin wadanda suka jagoranci tafiyar CPC.

Masu uwa da makarbiya a APC a yankin Arewa maso tsakiya sun yi zama a ranar Lahadin da ta wuce a Ilorin, jihar Kwara, inda suka dauki wannan matsaya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zaben APC
Shugabannin APC na kasa Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Dalilan goya masa baya

‘Yan North Central APC Central Advisory Council sun bayyana cewa hankalinsu ya fi kwanciya da Mustapha domin shi ne ya cancanta da rikon jam’iyyar.

Legit.ng ta ji cewa ‘ya ‘yan jam’iyyar APC sun gamsu da Mustapha ne saboda shi ne zai iya hada-kan kowa, kuma babu kazantar rashin gaskiya tattare da shi.

Ambasada Christopher Ameh wanda ya jagoranci ‘ya ‘yan APC daga Benuwai ya ce Mustapha ne suke ganin ya fi kowa dacewa ya zama shugaban jam’iyyarsu.

Kara karanta wannan

Yadda yunkurin zawarcin Jonathan, a ba shi takara a APC ya sha ruwa tun kafin a kai 2023

Tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Kwara, Fasto Benjamin Yisa wanda shi ya kira wannan taro ya ce sun yi la’akari da kuruciya da gaskiyar Mustapha.

Jigon APC a jihar Nasarawa, Ahmed Goringo ya ce tun a zamanin The Buhari Organisation (TBO) ake tara da Saliu Mustapha, kafin Buhari ya samu shugabanci.

Tinubu ya na goyon bayan Sani Musa

A baya an ji cewa kusan mutum hudu ne a gaba yanzu wajen neman zama shugaban jam’iyyar APC. Daga ciki akwai Tanko Al-Makura da Abdullahi Adamu.

Rahotanni su na nuna cewa jagoran APC, Bola Tinubu yana tare ne da Sani Musa. Da alamu sai Sanata Sani Musa ya yi da gaske a zaben da za ayi a watan gobe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng