Gwamnoni sun tsaida matsaya kan zaben shugabanni da makomar Buni a taron Abuja

Gwamnoni sun tsaida matsaya kan zaben shugabanni da makomar Buni a taron Abuja

  • Gwamnoni kimanin 20 na jam’iyyar APC suka hadu a gidan shugaban gwamnonin APC na kasa
  • A wannan zaman da aka yi a birnin tarayya Abuja, an tsaida magana a kan zaben shugabanni na kasa
  • Shugaban gwamnonin APC, Abubakar Atiku Bagudu ya ce maganar zabe na nan a watan Fubrairu

Abuja - Akalla gwamnoni 20 na jam’iyyar APC mai mulki suka yi zama a bayan labule a gidan gwamnatin jihar Kebbi da ke Asokoro, birnin Abuja.

Wani rahoton da Vanguard ta fitar ya ce ba a kammala wannan zaman a ranar Lahadi, 16 ga watan Junairu, 2022 sai da kimanin karfe 11:30 na dare.

Kan gwamnonin jam’iyyar mai mulki ya rabu a kan ko za a janye zaben shugabanni na kasa da aka tsara, ko kuwa zai wakana ne a watan na Fubrairu.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa na yarda zan lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Tinubu

A karshen wannan taro, shugaban gwamnonin APC na kasa, Abubakar Atiku Bagudu ya ce kungiyarsu ta nuna goyon bayanta ga kwamitin Mala Buni.

Mai girma gwamnan Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu ya ce jam’iyyar APC za ta gudanar da zaben shugabannin na ta na kasa kamar dai yadda aka tsara.

Gwamnoni
Gwamnonin APC a wani taro Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Mai Mala Buni ya tsira

Hakan ya na zuwa ne a lokacin da ake ta rade-radin cewa wasu gwamnoni ba su tare da Buni.

Kwamitin rikon kwaryan da Gwamnan Yobe, Mala Buni yake jagoranta yana dauke da wasu gwamnonin biyu; Abubakar Sani Bello da Gboyega Oyetola.

Gwamna Atiku Bagudu bai bayyana takamaimen ranar da za ayi zaben a watan na Fubrairun ba.

Jaridar ta ce sai dai shugaban gwamnonin na jam’iyyar APC ya ce kwamitin rikon kwarya na CECPC zai tattauna da masu ruwa da tsaki domin sa rana.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Manyan kalamai 4 da gwamnan PDP yayi game da takarar Tinubu

Kwamitin CECPC na rikon kwarya ne zai tsara yadda babban zaben zai kasance da kuma yadda za a raba kujerun shugabanni na matakin kasa a jam’iyyar APC.

Gwamnonin da suka je taron

Gwamnonin da aka yi wannan zama da su sun hada da: Dapo Abiodun (Ogun), Rotimi Akeredolu (Ondo), Nasir El-Rufai (Kaduna), da Yahaya Bello (Kogi).

Sai kuma Abubakar Sani Bello (Neja), Mohammed Abubakar Badaru (Jigawa), Bello Matawalle (Zamfara), Dave Umahi (Ebonyi), Babagana Zulum (Borno).

Ragowar su ne Gboyega Oyetola (Osun), Babajide Sanwoolu (Legas), Simon Bako Lalong (Filato), Abdullahi Sule (Nasarawa), sai shi Mai Mala Buni (Yobe).

An ji cewa taron ya samu halartar Hope Uzodinma (Imo), Dr. Ben Ayade (K/Riba), Abdulrahman Abdulrazaq (Kwara), Farfesa Babagana Zulum (Borno), Dr. Abdullahi Umar Ganduje (Kano), Abubakar Atiku Bagudu (Kebbi) da Kayode Fayemi (Ekiti).

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng