Atiku, Kwankwaso sun tsaya wasa, ‘Yan siyasa 2 sun bayyana niyyar tsayawa takara a PDP

Atiku, Kwankwaso sun tsaya wasa, ‘Yan siyasa 2 sun bayyana niyyar tsayawa takara a PDP

  • Sam Ohuabunwa ya sanar da shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr. Iyorchia Ayu shirin da yake yi
  • Ohuabunwa zai nemi tikitin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar hamayya a zaben 2023
  • Hakan na zuwa ne bayan Dele Momodu ya bada irin wannan muhimmiyar sanarwa a ofishin PDP

Fitaccen masanin nan wanda ya kware wajen harkar hada magunguna, Sam Ohuabunwa ya sanar da jam’iyyar PDP game da burinsa na neman shugabanci.

Jaridar Premium Times ta ce Sam Ohuabunwa ya bayyana wannan shirin da yake da shi ne a wata takarda da ya aikawa shugaban jam’iyyar PDP, Iyorchia Ayu.

Da yake zantawa da manema labarai bayan zaman su a sakatariyar PDP, Ohuabunwa yace neman takara sai da koshin lafiya, tsare-tsare, da sanin kan makaman aiki.

Wasikar Ohuabunwa ta shiga hannun Dr. Ayu a ranar Alhamis, 13 ga watan Junairu, 2022.

Kara karanta wannan

Hular Tinubu ta yi daraja a kasuwar intanet, 'yan Najeriya sun yi tururuwa domin saye

“Ofishin shugaban kasa ba wasa ba ne. Dole ya zama ka san kan aiki, ka kuma rike mukamai da-dama a tarihi.”
“Na san kan aiki, kuma na samu horo. Watakila ina cikin rukunin tsofaffi, amma jiki na, na yaro ne har abada.”

- Sam Ohuabunwa

Sam Ohuabunwa
Sam Ohuabunwa Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: Facebook

Manufa ta - Ohuabunwa

Mista Ohuabunwa ya ce idan ya samu damar zama shugaban kasa, gwamnatinsa za ta rika auna kokarin da kowa yake yi domin ayi masa sakayyar da ta dace da shi.

Idan mulki ya fada hannun Ohuabunwa a PDP, yace zai kokarta wajen ba kowa dama a kasar nan, ta yadda zai cin ma burin rayuwa kamar yadda ake yi a Amurka.

Dele zai jarraba sa'a

Ohubunwa wanda ya taba zama shugaban kungiyar Nigerian Economic Summit Group (NESG) ya sanar da PDP hakan ne bayan an ji Dele Momodu ya ce zai yi takara.

Kara karanta wannan

Fitaccen dan jarida, Dele Momodu ya ayyana kudurin tsayawa takara a 2023 a PDP

Mawallafin mujallar Ovation Magazine, Momodu ya shaidawa Ayu cewa zai yi takara a zaben 2023.

Sauran mutanen kudu maso gabas masu sha’awar takarar shugaban kasa su ne Anyim Pius Anyim, Kingsley Moghalu, Sanata Orji Uzor Kalu, sai Dave Umahi.

Takarar Ovie Omo-Agege

A wani lamari kamar da karfi da yaji, Enyen-Nyen Movement ta ce dole Ovie Omo-Agege ya fito ya nemi takarar kujerar gwamnan jihar Delta a zabe mai zuwa na 2023.

Idan har Sanata Ovie Omo-Agege ya ki amsa kiran ‘yan tafiyar Enyen-Nyen Movement nan da watan Afrilu, za su kai karar shi zuwa kotu domin ayi shari'a da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng