Burin Tinubu ya gamu da cikas na farko, Shugaban Yarbawan Afenifere ya ki mara masa baya

Burin Tinubu ya gamu da cikas na farko, Shugaban Yarbawan Afenifere ya ki mara masa baya

  • Shugaban kungiyar Yarbawa na Afenifere ya tofa albarkacin bakinsa a kan takarar Bola Tinubu
  • Cif Ayo Adebanjo ya ce tsohon gwamnan jihar Legas zai iya tsayawa neman mulkin Najeriya a 2023
  • Adebanjo ya bayyana cewa ba za su tofawa takarar Tinubu albarka ba sai an canza tsarin mulki

Shugaban kungiyar Yarbawa na kasa watau Afenifere, Ayo Adebanjo ya yi martani a game da shirin Asiwaju Bola Tinubu na takarar shugaban kasa.

Cif Ayo Adebanjo ya bayyana cewa kungiyar Afenifere ba za ta marawa wani ‘dan takara daya baya ba, har sai an canza tsarin mulkin kasar kafin 2023.

Adebanjo ya ce ba su yarda da tsarin mulkin da ake amfani da shi ba, don haka suke bukatar ayi gyara. Daily Trust ta fitar da wannan rahoto a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Na shirya yin gaba da gaba da Tinubu a zaben fidda gwanin APC – Shahararren sanata

A game da burin Asiwaju Bola Tinubu na tsayawa takara a zabe mai zuwa, dattijon mai shekara 93 ya ce ‘dan siyasar ya na da ‘yancin ya nemi shugabanci.

Ya na da damar takara - Adebanjo

“Mutuminku yana da duk wata damar shiga takara, bai da nakasa, saboda haka menene abin magana a kai?

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban Afenifere
Jagaban Bola Tinubu da Cif Ayo Adebanjo Hoto: www.naijanews.com
Asali: UGC

Ba mu amince da tsarin mulki ba

“Ba mu neman kujerar shugaban kasa a yanzu, saboda ba mu yarda da tsarin mulkin da muke da shi ba.”
“Sai an canza wannan tsarin mulki, sannan za mu yi magana a kan daga ina ya dace a samu shugaban kasa.”
“Ba mu da ‘dan takara a yanzu haka, sai an sauya tsarin mulkin kasar, ba za mu shiga inda babu tsari ba.”
“Dole ka yarda da tsarin mulkin kasar kafin ka ce za ka shiga ciki a dama da kai, ba na cikin wannan.”

Kara karanta wannan

Tuna baya: Wata 2 da suka gabata, Fashola yace Tinubu zai bayyana burinsa a watan Janairu

“Babu ruwa na da zaben da zai yi aiki da tsarin mulkin da sojoji suka yi. Maganar mu kenan.” – Adebanjo.

Daily Post ta rahoto Adebanjo yana cewa ko shugaba Muhammadu Buhari ya yarda cewa tsarin mulkin sojoji ne gwamnatin Najeriya take amfani da shi.

Fayemi ya ziyarci Tinubu

A jiyan ne dai aka ji cewa Kayode Fayemi ya je har gida ya samu Asiwaju Bola Tinubu, sun tattauna a kan muhimamman batutuwan da suka shafi siyasa.

Gwamna Kayode Fayemi ya zauna da Tinubu bayan ya ayyana niyyar takara a 2023, sannan kuma APC ta na shirin tsaida 'dan takarar gwamna a jihar Ekiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng