Tarihin Marigayi Shonekan wanda ya yi kwana 83 a mulki, Abacha ya yi masa juyin-mulki

Tarihin Marigayi Shonekan wanda ya yi kwana 83 a mulki, Abacha ya yi masa juyin-mulki

  • A ranar Talata, 11 ga watan Junairu, 2022 ne Cif Ernest Adegunle Oladeinde Shonekan GCFR ya rasu
  • Marigayi Ernest Adegunle Oladeinde Shonekan ya rike mulki na ‘yan kwanaki kadan a Najeriya
  • Tsohon shugaban kasar bai cika watanni uku a mulki ba, sai Janar Sani Abacha ya hambarar da shi

Me ka sani game da rayuwar Ernest Shonekan GCFR?

1. An haifi Ernest Shonekan ne a ranar 8 ga watan Mayu, 1936, ya rasu saura watanni hudu ya yi bikin cika shekaru 86 da haihuwa kenan a Duniya.

2. Legit.ng Hausa ta samu labari cewa an haifi Marigayin ne a garin Ogun, ya rike sarautar Abese na kasar Egba, kuma yana auren Margaret Shonekan.

3. Tsohon shugaban kasar na rikon kwarya ya yi karatun ilmin shari’a ne a jami’a. Bayan ya zama Lauya sai ya shiga harkar kasuwanci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi: Tsohon shugaban kasa a Najeriya Ernest Shonekan ya rasu

4. Cif Ernest Shonekan ‘dan kasuwa ne wanda ya rike katafaren kamfanin United African Company of Nigeria wanda ake ji da shi a Afrika a lokacin.

5. Marigayin ya fara aiki da kamfanin UAC ne a shekarar 1964. Kafin ya bar kamfanin sai da ya shiga cikin majalisar Darektoci yana 'dan shekara 40.

6. Bayan ya zama Darekta a United African Company of Nigeria a shekarar 1980, sai ya shiga wasu harkokin kasuwanci da siyasar kasashen Duniya.

7. Bayan an soke zaben 1992, sai Janar Ibrahim Babangida ya sauka daga karagar mulki, ya zabi Shonekan ya zama shugaban kasa na rikon kwarya.

8. A watan Agustan 1993 ne aka rantsar da Shonekan a matsayin Shugaban kasa na rikon kwarya, ya canji Babangida wanda ya ke mulki tun 1985.

Kara karanta wannan

Yadda Kano ta rasa ‘Yan siyasa, ‘Dan kasuwa, Saraki, Malami, da wasu manya 8 a kwana 53

9. Shonekan ya rike Gwamnatin tarayya a lokacin Najeriya ta na tangal-tangal da fama da bashi, sai da ta kai ya kara farashin man fetur kafin ya sauka.

10. Gwamnatin Shonekan tayi kokarin shawo kan matsalar siyasar da kasar ta samu kan ta tun bayan da Sojoji suka soke zaben MKO Abiola da Bashir Tofa.

Shonekan
Abdussalami, Marigayi Shonekan, da Obasanjo Hoto: www.nairaland.com
Asali: UGC

11. Shonekan ya yi kokarin fito da mutanen da Babangida ya daure. Sai dai mulkinsa ya gamu da cikas, inda kotu ta warware ingancin gwamnatinsa.

12. Yayin da yake kan kujerar shugaban kasa a shekarar 1993, Marigayi Ernest Shonekan ya rike mukamin a kamfanin mai na Royal Dutch Shell.

13. Cif Shonekan ya samu matsala da Ministan tsaro kuma shugaban hafsun tsaro da Janar Babangida ya bari a kan mulki da ya tafi, Marigayi Janar Sani Abacha.

14. A karshe Janar Sani Abacha ne ya tursasawa Shonekan yin murabus da karfi da yaji a Nuwamban 1993. Kwanaki 83 kacal ya yi yana kan karagar mulki.

Kara karanta wannan

Buhari ya tuno tsohuwar alaka, ya rabawa iyalin abokansa da suka mutu mukamai a NNPC

15. Bayan ya sauka daga kan kujerar shugaban kasa, Shonekan ya kafa kungiyar Nigerian Economic Summit Group a 1994 ta masana tattalin arziki.

Buhari ya kafa tubali

A jiya ne hadimin shugaban Najeriya, Bashir Ahmaad ya ce turbar da Shugaba Muhammadu Buhari ya ɗauka ba za a ga amfaninta a fili ba sai bayan ya bar mulki.

Hadimin shugaban kasar yace dama wasu tsare-tsaren na gyara ba sa yiwuwa sai an sha wuya, amma daga karshe za a ci moriyarsu, kuma a lokacin za a yaba masu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng