Zaben shugabannin jam’iyyar APC ya jawo sabani, kan Gwamnonin Jihohi ya rabu gidaje 3

Zaben shugabannin jam’iyyar APC ya jawo sabani, kan Gwamnonin Jihohi ya rabu gidaje 3

  • A watan gobe ake sa rai kwamitin Gwamna Mai Mala Buni zai shirya zaben shugabannin APC na kasa
  • Sai dai a daidai wannan lokaci, babu hadin-kai tsakanin Gwamnonin jihohin da ke karkashin APC
  • Gwamnonin sun bangare inda wasu suke goyon bayan Tinubu, wasu na tare da wani abokin aikinsu

Abuja - Gwamnonin da ke karkashin jam’iyyar APC mai mulki sun samu kansu a rabe. Daily Trust ce ta fitar da wannan rahoton a ranar 11 ga watan Junairu, 2022.

Abin da ya jawo sabanin da aka samu shi ne lokacin da za a zaba domin shirya zaben shugabannin jam’iyya na kasa wanda ake sa rai za ayi a Fubrairu.

A karshen shekarar 2021, wasu shugabannin jam’iyyar suka yi zama da Muhammadu Buhari inda aka amince ayi zaben a Fubrairu, amma ba a tsaida rana ba tukuna.

Kara karanta wannan

Jonathan ya gamu da sarkakiya a titin 2023, Jiga-jigan APC ba su gamsu da sauya-shekarsa ba

A halin yanzu wasu daga cikin ‘ya ‘yan APC sun huro wuta, su na so kwamitin rikon kwaryan da Mai Mala Buni yake jagoranta, ya sake daga lokacin yin zaben na kasa.

An dakatar da zaman gwamnoni

Wata majiya ta shaidawa Vanguard cewa sabanin da aka samu tsakanin gwamnonin ya jawo aka daga zaman da aka shirya za ayi a ranar Lahadin da ta gabata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugabannin jam’iyyar APC
Mai Mala Buni da Buhari Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Yayin da ake sa ran ayi zaben a watan gobe, akwai gwamnonin jihohin da ba su gamsu da hakan ba. Har yanzu kuma an gagara samun yadda kan su zai hadu.

An samu bangarori uku

Jackson Lekan Ojo yace a cikin gwamnonin APC akwai wadanda ke goyon bayan Tinubu, sannan akwai bangaren wani gwamna da yake harin shugaban kasa.

“Gwamnonin APC sun rabu bangare uku. Wasu na tare da Bola Tinubu, wasu su na tare da wani kusa a fadar shugaban kasa."

Kara karanta wannan

Ka yi daidai: Shehu Sani ya goyi bayan Buhari kan watsi da batun 'yan sandan jiha, ya fadi dalili

Wasu kuma na tare da wani gwamnan Arewa maso tsakiya da yake da niyyar tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023."

- Jackson Lekan Ojo

Har yanzu ba a sanar da INEC ba

A ka’ida ya kamata APC ta sanar da INEC shirin yin zaben shugabannin akalla makonni uku kafin lokaci. Har zuwa yanzu jam’iyyar ba ta aikawa INEC takarda ba.

Chekwas Okorie ya shaidawa Daily Trust cewa zai yi wahala a iya yin zaben shugabanni a Fubrairu.

Gwamnan APC ya koka

A makon jiya aka ji Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, yace wasu abokan adawarsa sun yi taron dangi domin bata masa suna saboda shirin takarar Shugaban kasa.

Duk da bai bayyana niyyarsa ba, Gwamna Kayode Fayemi yace babu dokar da ta hana shi tsayawa takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng