Da Dumi-Dumi: Jiga-Jigan APC sun bukaci Kotu ta dakatar da gangamin taron APC na ƙasa
- Wasu mambobin jam'iyya mai mulki sun garzaya kotun tarayya a Abuja, sun bukaci ta dakatar da gangamin APC na ƙasa
- A cewarsu, APC ba ta kammala zaben shugabanninta na matakin jihohi ba, kuma akwai rigingimu a gaban kotu
- Jam'iyyar APC, shugaban kwamitin rikon kwarya, Gwamna Mala Buni, da hukumar INEC sune waɗan da mambobin suka shigar ƙara
Abuja - Fusatattun mambobin jam'iyyar APC sun bukaci babbar kotun tarayya dake Abuja, ta dakatar da kwamitin rikon kwarya na Mala Buni daga gudanar da babban taro na ƙasa a watan Fabrairu.
Mambobin da suka shigar da ƙarar sune, Suleiman Usman, daga Abuja, Muhammed Shehu, daga Zamfara da kuma Audu Emmanuel, daga Zamfara, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
A ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/3/2022, da lauyansu, Olusola Ojo, ya shigar, mambobin sun ce jam'iyyar APC na shirin saɓa wa dokokin ta idan aka bari ta gudanar da taron a Fabariru.
Ƴaƴan jam'iyya mai mulki sun kafa hujja da cewa kasancewar APC ba ta kammala zaɓukan shugabanni a matakin jihohi ba, bai kamra ta yi taron ƙasa ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Waɗan da mambobin suka shigar ƙara sune, jam'iyyar APC, shugaban kwamitin rikon kwarya, gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe, da kuma INEC.
Wane jihohi ne APC ba ta gudanar da zabe ba?
Masu shigar da karar sun bayyana cewa APC ta gudanar da zaɓukan shugabanni a dukkan jihohi ranar 16, ga watan Oktoba, 2021, amma banda Anambra da Zamfara.
Channels ta rahoto wani sashin jawaban masu kara da cewa:
"Bayan tarukan jihohi da suka gudana a watan Oktoba, wasu mambobi da yan takara da suka fafata a zabuka daban-daban sun shigar da APC ƙara a gaban kotu."
"'Yayan jam'iyya sun kalubalanci yadda aka gudanar da zabuka bisa murɗiya da kuma watsi da dokokin jam'iyya da na zaɓe."
"Ba tare da kammala zaben shugabannin jihohi ba da kuma warware rigingimun dake gaban kotu, APC da Mala Buni sun cigaba da shirin babban taro na ƙasa."
Bisa wannan dalili ne, masu shigar da karar suka bukaci kotu ta dakatar da babban taron APC na ƙasa, domin gudanar da shi ya saba wa kundin dokokin da aka kafa jam'iyyar da su.
A wani labarin na daban kuma Mambobin jam'iyyar PDP 4,000 zasu sauya sheka zuwa APC mai mulki a Jigawa
Jam'iyyar APC reshen jihar Jigawa dake Arewa maso yammacin kasar nan tace nan ba da jimawa ba zata karbi mambobin PDP 4,000.
Shugaban APC a Jigawa, Sani Gumel, yace masu sauya shekan sun ɗauki matakin dawowa APC ne saboda kyakkyawan jagoranci.
Asali: Legit.ng