Da an ji kunya: Bai dace APC ta ba Jonathan takarar shugaban kasa ba - Tsohon Hadimin Buhari
- Hon. Abdurrahman Kawu Sumaila ya soki masu neman a ba Dr. Goodluck Jonathan takara a APC
- Tsohon ‘dan majalisar tarayya mai wakiltar Takai da Sumaila yace APC ba ta rasa ‘yan takara ba
- Sumaila yana ganin Jonathan ya cancanci a yaba masa, amma duk da haka bai dace da tutar APC ba
Kano - Tsohon ‘dan majalisar tarayya, Hon. Abdurrahman Kawu Sumaila yace makiyan APC ne suke shirin ba Goodluck Jonathan takarar jam’iyya a 2023.
Daily Trust ta rahoto Honarabul Abdurrahman Kawu Sumaila yana cewa tsohon shugaban Najeriyar ya yi iya yinsa, ya kamata a kyale shi ya huta kuma.
Kawu Sumaila ya na ganin jam’iyyar APC ta na da ‘yan takarar shugaban kasa daga kudancin Najeriya da suka fi Goodluck Jonathan cancanta da samun tikiti.
Jita-jita na yawo cewa wasu manyan APC na so a tsaida Jonathan takarar shugaban kasa a 2023.
Sumaila wanda ya yi aiki a matsayin mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kan harkokin majalisar tarayya ba ya goyon bayan wannan ra’ayin.
Jonathan ya cancanci yabo, amma...
Vanguard ta rahoto Hon. Sumaila yana yabon Jonathan, yace amma idan APC tace shi za ta mikawa tuta a zaben 2023, ta na nufin ta rasa ‘dan takara kenan.
“Ba na tunanin masu dagewa a kan sai Jonathan ya gaji Muhammadu Buhari a karkashin jam’iyyarmu su na neman APC da zaman lafiya.”
“Goodluck Jonathan ‘dan siyasa ne da ya cancanci jinjina, wanda ya san tsarin damukaradiyya.”
“Amma ya taka rawarsa a karkashin jam’iyyar PDP, babu wanda ya isa ya ja da cewa ya mika mulki ga jam’iyyar hamayya a cikin ruwan sanyi.”
“Maganar gaskiya ya fi wasu da yawa a jam’iyyarmu. Sai dai ba za mu ce Jonathan ya zo mu ba shi tikiti bayan akwai wasu ba, mun gaza kenan.”
- Hon. Abdurrahman Kawu Sumaila
Wanene 'dan takarar Buhari?
Mai girma Shugaban Najeriya ya ki kama sunan ko daya a cikin jiga-jigan APC, yace babu abin da ya dame shi da 2023 domin shi dai ya gama na shi.
Muhammadu Buhari yana ganin idan ya ambaci ‘Dan takararsa a zabe mai zuwa na 2023, to tabbas ba zai kai labari ba, za ayi masa taron-dangi
Asali: Legit.ng