"Yadda Gwamna mai-ci ya bada umarni a nemi ayi wa ‘Dan takarar Gwamna kusan zindir"

"Yadda Gwamna mai-ci ya bada umarni a nemi ayi wa ‘Dan takarar Gwamna kusan zindir"

  • Mista Uche Nwosu ya bada labarin irin cin mutuncin da jami’an tsaro suka yi masa da suka kama shi
  • ‘Dan takarar gwamnan Imo na jam’iyyar AA a zaben 2019 yace Hope Uzodinma ya sa aka cafke shi
  • Gwamnatin jihar Imo ta musanya wannan zargin ta bakin Declan Emelumba, tace ba gaskiya ba ne

Imo - ‘Dan takarar jam’iyyar AA a zaben 2019 a jihar Imo, Uche Nwosu, ya yi magana game da cafke shi da jami’an tsaro suka yi a coci a makon jiya.

Da yake bayanin abin da ya faru, Daily Trust ta rahoto Uche Nwosu ya na cewa Hope Uzodinma ne ya yi kutun-kutun, har jami’an tsaron suka kama shi.

Surukin na tsohon gwamna Rochas Okorocha ya bayyana wannan ne da ya zanta da ‘yan jarida a ranar Talata, 28 ga watan Disamba, 2021 a garin Owerri.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta yi magana a kan cafke sirikin tsohon gwamna a wurin Ibada

A cewar Nwosu wanda ya yi takara da Uzodinma, burin gwamnan mai-ci shi ne a hallaka shi. Nwosu ya godewa IGP da ya sa baki har aka fito da shi.

Nwosu yace bayan an cafke shi a coci a garin Eziama Obaire, sai aka wuce da shi filin jirgin jihar Enugu, daga nan ya samu kan shi a birnin tarayya Abuja.

‘Dan takarar Gwamna Imo
Mr. Uche Nwosu Hoto: www.sunnewsonline.com
Asali: UGC

‘Dan siyasar yace Gwamna Uzodinma ya yi amfani da jami’an tsaron da ke gidan gwamnati wajen kama shi da ci masa mutunci domin a iya ganin bayansa.

Nwosu ya zargi mai girma Uzodinma da ba jami’an tsaro umarni su tube masa tufafi, yace bayan an kama shi, an turawa gwamna bidiyon halin da yake ciki.

Bayan an buda wuta yayin da ake huduba a coci, an dauke shi aka shigar da shi cikin wata mota inda ya ji jami’an tsaron su na magana da harshen Hausa.

Kara karanta wannan

Okorocha ya fadi mutane 2 da ke da hannu wajen ba ‘Yan Sanda umarnin cafke surukinsa

Da yake ya na jin Hausa, Nwosu yace ya ji ana magana da wani jami’in tsaro da ke gidan gwamnan Imo, yace an nemi a kashe shi da aka isa garin Umuaka.

“Sun bukaci in cire kayan jiki na, su ka daure mani hannu, suka dauki hoto na, suka yi mani bidiyo, suka turawa babban mai tsaron gwamna.” - Nwosu

Punch tace kwamishinan yada labarai da dabaru na Imo, Declan Emelumba yace babu ruwan gwamna ko gwamnati da kama Nwosu kamar yadda yake fada.

Aikin Gwamna Hope Uzodinma ne - Okorocha

Kwanaki aka ji tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha ya yi kaca-kaca da Gwamna Hope Uzodinma a dalilin kama surukinsa da aka yi a wajen ibada.

Sanata Okorocha yace Hope Uzodinma ne ya sa Sufetan 'Yan Sandan Najeriya ya bada umarni a cafke Uche Nwosu bayan an yi masa sharrin tada zaune tsaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng