Siyasar Kano: Maganar sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje ta jawo ana ta ce-ce-ku-ce

Siyasar Kano: Maganar sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje ta jawo ana ta ce-ce-ku-ce

  • Legit.ng ta fahimci cewa ta’aziyyar da gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kai wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta bar baya da kura
  • Yayin da wasu suke ganin gaisuwa gami da roƙon iri ta kai Abdullahi Umar Ganduje gidan tsohon mai gidan na sa, wasu na ganin zumunci ne kurum
  • A gefe, wasu na cewa dama sun san zuwa gaisuwar da biyu, musamman bayan an ji Ahmad Sulaiman Ibrahim ya karanta ayar sulhu a wajen gaisuwa
  • Su kuma magoya bayan gwamna sun ce wannan ya nuna Dr. Ganduje yana siyasa ne ba da gaba ba, har ya je ya yi wa Kwankwaso gaisuwar mutuwa

Legit.ng Hausa ta tattaro abubuwan da wasu daga cikin masu bibiyar siyasar Kano da ‘yan Kwankwasiyya da tsagin gwamna Ganduje ke fada a Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yi bayani kan shirin gwamna Ganduje na ficewa daga jam'iyyar APC

Salisu Yahaya Hotoro ya bayyana ra’ayinsa, yace dole ce ta sa Ganduje zuwa gaisuwar, yace idan mai gidansa, Kwankwaso ya amince ayi sulhu, to zai yi biyayya.

"Allah sarki Modibbo, Wallahi ya fara bani tausayi. Watau ya lura dare yana neman yi masa a dawa, sai ya lallabo gida."
“Ni idan ana Maganar siyasa bani da zaɓi, abin duk da Madugu yake so shine zaɓi na saboda nayi imani ba zai taɓa tuƙani ya kaini ramin da ba zan iya fitowa ba. Bani da wani buri ko bukata a siyasa da ya wuce naga burin Kwankwaso da buƙatarsa sun cika.”
- Salisu Yahaya Hotoro

Hon Musayyib Kawu Ungogo ya rubuta:

“Ni dama na san zuwa gaisuwar nan akwai wata a kasa. Yanzu dai gashi gwamna da kansa na maganar sulhu da tsohon mai gidan sa.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Sanata Kwankwaso ya yi magana game da ta’aziyyar da Ganduje ya zo ya yi masa har gida

“Ni fa in dai ana so sulhun nan ya tabbata saidai a sauke Musa Iliyasu Kwankwaso a bani kujerar sa. Shine zance na gaskiya.”

Shi ma Yusuf Abubakar Babati, cikin ba’a yace dole a ba shi mukami, muddin ana so ayi sulhu.

“In dai za a cire Ali Baba a bani kujerar sa Allah ya sulhunta.”
Kwankwaso da Ganduje
Sanata Rabiu Kwankwaso da Gwamna Ganduje Hoto: @mohd.saifullahi.9
Asali: Facebook

Ra’ayin Abdulaziz Tijjani

"A dai sanin da na yi wa Ganduje, na tabbatar wannan yunkurin nasa na daidaitawa da Madugu (Rabiu Kwankwaso) kawai kiran lamba yake yi wa uwar jam'iyya."
"Dukkan alamu sun nuna Madugu yana kaunar Ganduje. Mu dai muna kungiyar sulhu alkhairi ne. Duk kuma matakin da madugu ya dauka mu shine daidai a wurinmu."

Shi kuwa Kabiru Dakata ya na ganin Mai girma gwamna ya makara wajen bijiro da batun sulhu a yanzu.

“Fir'auna ma ba saida ya ga zai halaka ba tukunna ya nemi sulhu?” - Kabiru Dakata.

Ta'aziyya ce ba komai ba - Aranposu

Kara karanta wannan

Ganduje: A Shirye Na Ke In Yi Sulhu Da Kwankwaso

Shugaban karamar hukumar Nasarawa, Auwal Lawan Shaaibu Aranposu ya sha ban-bam da abokan adawarsu, yace Ganduje ya sake nuna kwarewarsa a siyasa.

“Wai Daga Zuwa Ta’aziya, duk kun damu mutane da maganar Sulhu. Mufa irin wannan zumunci ba sabon Abubane awajenmu.”

- Auwal Aranposu

Me Kwankwaso ya fada game da gaisuwar Ganduje?

A ranar Laraba kun ji cewa tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso ya yi wa Dr. Abdullahi Ganduje da sauran wadanda su ka zo yi masa ta’aziyya godiya.

Daga baya sai aka ji Ganduje ya na cewa ya shirya sulhuntawa da tsohon mai gidansa. Tun daga 1999 zuwa 2015 su na tare, an samu sabani ne bayan zaben 2015.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng