Yadda Gwamnoni 6 suka hana Majalisa juyawa Shugaban kasa baya a kan kudirin gyara zabe

Yadda Gwamnoni 6 suka hana Majalisa juyawa Shugaban kasa baya a kan kudirin gyara zabe

  • Gwamnonin jihohi sun shawo kan ‘Yan majalisa, an janye batun tabbatar da kudirin gyara harkar zabe
  • Wasu Sanatoci sun yi niyyar shigo da dokar zabe ko shugaba Muhammadu Buhari ya so, ko bai so ba
  • Shugaban gwamnoni, Kayode Fayemi da Yahaya Bello su na cikin wadanda suka sa aka janye maganar

Abuja - ‘Yan majalisar tarayya sun fara shirin amfani da karfinsu domin tabbatar da kudirin zabe a matsayin doka, amma wannan yunkurin ya wargaje.

Daily Trust ta fitar da rahoto cewa wasu Gwamnoni sun shiga cikin wannan magana, hakan ya sa adadin kuri’un da Sanatoci suke bukata ya kara yin kasa.

Majiya mai karfi tace gwamnonin APC da na PDP sun kira ‘yan majalisunsu, inda su ka bukaci su ajiye batun warware matakin da shugaban kasa ya dauka.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Halaka Dan Sanda Da Wasu 22 Sannan Suka Kona Gidaje 50 A Wata Jahar Arewa

Gwamnonin sun fadawa ‘yan majalisar tarayyan cewa yin hakan zai zama cin fuska ga shugaba Muhammadu Buhari, don haka aka hakura da yunkurin.

A wani rahoto da jaridar The Nation ta fitar dazu, an ce wani babban gwamna na jam’iyyar APC ya dage wajen ganin hakar Sanatocin ba ta cin ma ruwa ba.

Shugaban kasa
Buhari da 'Yan Majalisar Tarayya Hoto: @Bashir Ahmad
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Maganar ta na tangal-tangal

Wani Sanata ya shaidawa manema labarai ba zai yiwu a janye matakin da shugaban kasa ya dauka ba domin ana bukatar sa hannun ‘yan majalisar wakilai.

A halin yanzu majalisar wakilan tarayya ta tafi hutu bayan ta amince da kundin kasafin kudin shekarar 2022, ba za ta dawo aiki ba sai a tsakiyar Junairu.

Har ila yau, akwai wani ‘dan majalisa da yace duk da yanzu an tafi hutu, maganar ta lafa ne kurum, da zarar an dawo za a yi kokarin tabbatar da kudirin.

Kara karanta wannan

2023: Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Dakatar Yakin Neman Zabe Kan Abu Ɗaya Da Ya Shafi Yan Najeriya

Su wane gwamnoni ne wannan?

The Nation tace gwamnan jihar Yobe kuma shugaban APC na rikon kwarya, Mai Mala Buni ne ya jagoranci gwamnoni wajen rushe shirin ‘yan majalisar.

Sauran gwamnonin da suka lallashi Sanatocin da ke da wannan shiri su ne: Kayode Fayemi, Atiku Bagudu, Yahaya Bello, Gboyega Oyetola da Hope Uzodinma.

Duka gwamnonin ‘yan jam’iyyar APC mai mulki ne kuma su na da ta-cewa a siyasar jihohinsu.

Buba Galadima da kudirin zabe

A jiya aka ji Buba Galadima ya ce hasashen shi ya tabbata game da kudirin gyaran zabe. Galadima yace sai da yace a fille masa kai idan Buhari ya yarda da kudirin.

Buba Galadima ya ce idan aka sa hannu a dokar zabe, ko kujerar kansila APC ba za ta ci ba, ya kalubalanci Buhari, yace idan ya isa, ya sa hannu a kudirin zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng