Babbar magana: Farfesa Soyinka yana so a tado maganar kisan Minista bayan shekaru 20

Babbar magana: Farfesa Soyinka yana so a tado maganar kisan Minista bayan shekaru 20

  • Farfesa Wole Soyinka ya roki Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya duba batun kisan Bola Ige
  • A makon nan ne cibiyar Bola Ige for Justice Centre ta shirya taro na musamman domin tuna shi
  • Shekaru 20 da suka wuce aka samu wasu ‘yan bindiga suka je gidan Ige a Ibadan, suka harbe shi

Babban marubucin Duniya, Farfesa Wole Soyinka, ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tado binciken kisan tsohon Ministan shari’a, Bola Ige.

A rana irinta yau, 23 ga watan Disamba, 2001, wasu mutane suka je har gidan Bola Ige, su ka buda masa wuta. Ige ya mutu ya na da shekara 71 a Duniya.

Jaridar Premium Times tace a wani sako da Farfesa Wole Soyinka ya aikawa ‘diyar marigayin, Funso Adegbola, ya yabi mahaifin na ta da aka hallaka.

Kara karanta wannan

Buhari: Sanatoci na kokarin hada-kai domin gyara dokar zabe da karfi da yaji ta Majalisa

A sakon na sa, Farfesan ya bayyana Marigayi Bola Ige a matsayin mutumin kwarai. An shirya wani taro a Legas domin cika shekara 20 da mutuwar Ige.

Vanguard tace cibiyar Bola Ige for Justice Centre ta shirya zama na musamman a ranar Talata, inda aka gabatar da lacca a game da tsarin damukaradiyya.

Farfesa Soyinka
Farfesa Wole Soyinka Hoto: dailypost.ng
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wole Soyinka ya yi kira ga Buhari

Wole Soyinka ya yi amfani da wannan dama, ya yi kira ga shugaban kasa ya farfado da binciken duk kashe-kashen da aka yi, da suke da nasaba da siyasa.

“Ko da cewa ana ganin babu bambanci tsakanin ran mutum, amma akwai wanda nauyinsu ya rataya musamman fa wadanda suke kan mulki.”
Ran Bola Ige a matsayinsa na Ministan shari’a na kasa, kuma ma’aikacin majalisar dinkin Duniya ya na cikin wadannan sahu.” – Wole Soyinka.

Kara karanta wannan

Wanda ya yi wa Buhari Minista a 1984 ya kawo shawarwarin yadda za a magance rashin tsaro

Zai yi kyau a gano masu laifi - Farfesa Soyinka

Farfesa Soyinka yake cewa akwai bukatar a dage wajen fallasa wadanda aka hada baki da su, da kuma ainihin wadanda suka hallaka wannan Bawan Allah.

Akwai bukatar ayi hakan saboda ayi adalci, a cewar Soyinka, wanda yake ganin idan aka cigaba da yin irin wannan ba a dauki mataki ba, za a shiga matsala.

Majalisa za ta nunawa Buhari karfinta?

Wasu Sanatoci su na neman nuna cewa ko shugaban kasa ya so, ko bai so ba, ‘sai an yi wa tsarin zabe garambawul kafin a fara aiki a kan kasafin kudin 2022.

Idan za a tuna, an taba yin lokacin da Sanatoci su ka shigo da dokar NDDC ta shekarar 2001 duk da shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ki rattaba hannunsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng