Bode George: Bisi Akande ya fito da littafin tarihinsa ne saboda saida takarar Bola Tinubu

Bode George: Bisi Akande ya fito da littafin tarihinsa ne saboda saida takarar Bola Tinubu

  • Bode George ya sake sukar littafin Bisi Akande watau ‘My Participation’, yace da biyu aka rubuta littafin
  • Jigon adawar yace babu abin da Cif Akande ya iya yi a wannan littafin sai wanke Asiwaju Bola Tinubu
  • George yace an rubuta My Participation ne saboda a saida Tinubu yayin da ake ganin an fara shirin zabe

Lagos - Bode George, daya daga cikin kusoshin jam’iyyar PDP, yace littafin ‘My Participation’ da ya fito kwanan nan, yunkurin saida takarar Bola Tinubu ne.

Jaridar The Cable ta rahoto tsohon mataimakin shugaban na jam’iyyar PDP ya na sukar littafin da Bisi Akande ya rubuta, yace da manufa biyu littafin ya fito.

Da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Arise TV a ranar Litinin, 20 ga watan Disamba, 2021, Cif Bode George yace an ci mutuncin kowa a wannan littafin.

Kara karanta wannan

Buhari bai ci amanar Tinubu a zabe ba – Jigon APC ya bayyana asalin abin da ya faru a 2015

Yayin da George yake zargin Bisi Akande da bata sunan manyan kasar, yace an wanke Tinubu da nufin a tallata shi a zaben shugaban kasa mai zuwa na 2023.

Abin da George ya fada

Bisi Akande
Buhari, Tinubu da Bisi Akande Hoto: @MBuhari
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Abin da kawai yake cikin littafin, wanda kurum aka yaba ba tare da an kushe shhi ba, shi ne Bola Bola Tinubu. Ba ku tunanin siyasa ce wannan?”
“Tinubu yana so ya fito takara (na shugaban kasa a zaben 2023), saboda haka dole ya yi duk abin da zai iya domin ya tallata shi.” – Bode George.

Yace fito da littafi makonni gabanin 2022 – ‘shekarar zabe a kasar nan’ – ya tabbatar da wannan.

“Yau mu na 20 ga watan Disamba, nan da wani watan mun shiga wata shekarar, a cikin mako daya. Kuma shekarar zabe kenan a kasar nan.”

Kara karanta wannan

Takarar 2023 na neman raba kan Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo da Ubangidansa Tinubu

“Daidai lokacin da za a fara tonon silili kenan, ana neman batawa wasu shugabanni suna, sannan ka wanke ‘danuwanka (Tinubu)” - Bode George.

Tsohon gwamnan yace idan ba siyasa ba, menene zai sa a gudanar bikin kaddamar da wannan littafi a garin Legas, tun da marubucin mutumin jihar Osun ne.

Littafin Akande ya jawo magana

Tun da aka kaddamar da wannan littafi, ake samun masu suka da masu martani suna ta magana. A baya, Bode George ya ba Akande shawarar ya janye littafin.

Daga cikin wadanda aka tabo a littafin ‘My Participation’, akwai Mai girma Muhammadu Buhari da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng