Manyan jiga-jigan PDP da daruruwan mambobi sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki
- Wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar PDP da magoya bayansu sun sauya sheka zuwa APC a jihar Cross River
- Gwamnan jihar Ben Ayade, yace babu kowa a jam'iyyar PDP ta jihar, tsagin adawa ya mutu murus
- Gwamnan ya kuma tabbatar wa mutanen jiharsa cewa za'a cigaba daga inda aka tsaya kan mulkin karba-karba da aka fara tun 1999
Cross River - Jiga-jigan PDP tare da dandazon magoya bayansu daga mazaɓar sanata ta kudancin jihar Cross Ribas sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC ranar Alhamis.
Da yake jawabi a wurin taron karɓan masu suaya sheka, Gwamna Ben Ayade na jihar Cross Riba, yace maganar tsarin mulkin karba-karba da aka fara a jihar tun 1999 yana nan daram.
Punch ta ruwaito cewa matukar aka cigaba da tsarin, yankin kudancin jihar ne zai fitar da gwamna na gaba a shekarar 2023.
Ayade ya misalta PDP da wata jam'iyyar da ta tafka asara, ya kuma kara da cewa ya zama wajibi a kansa ya tabbatar cewa al'ummarsa sun guje ta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Vanguard ta rahoto Gwamnan yace:
"Ba halina bane ba, zan cika akawari. Shekarar 2023 lokaci ne na zaman lafiya, daidaito da adalci saboda kowa yasan ana yi da shi, kuma mu rinka baiwa kowa hakkinsa a siyasa."
"Wannan zai baiwa kowa dama yasan an zo kansa a lokacin da ya dace. Idan na duba tarihin Cross Ribas ina mamakin daga ina tsagin hamayya ke fitowa."
"Jam'iyyar PDP ta mutu, babu komai a cikinta. Jam'iyyar APC ce ke jan ragama yanzu, duk mai son cigaba da ganin mu a bangaren adawa to ba ya mana fatan alheri."
Gwamnan ya kuma bayyana cewa jam'iyyar APC ta samu gurin zama a jihar Cross Ribas, kuma an samu banbanci tsakanin lokacin baya da kuma yanzu.
"Waɗan da suka gina PDP kuma suke tafiyar da ita, sune ke dawo wa cikin mu a APC yau. Me kuma ya yi saura a PDP ta Cross Ribas? ta mutu kawai."
A wani labarin na daban kuma Tsohon gwamnan Kaduna, Ramalan Yero, Ya bayyana shirinsa na tsayawa takara a zaben 2023
Tsohon gwamnan Kaduna, Ramalan Yero, yace a halin yanzun wuƙa da nama na hannun mutane su tantance tsakanin PDP da APC.
Yero, wanda ya sha kaye a hannun El-Rufai a 2015, yace mutane sun gwada PDP na shekara 16, sun kuma gwada APC na shekara 8.
Asali: Legit.ng