Akande: Tsohon Shugaba Obasanjo ya karya kowa, Tinubu kadai ya gagare shi a 2003 – Buhari
- Bisi Akande ya rubuta littafin tarihinsa wanda har Muhammadu Buhari ya samu zuwa kaddamarwa
- Cif Akande ya yi wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo kaca-kaca a wannan littafin da ya rubuta
- Shugaba Buhari ya soki Obasanjo a littafin, inda yace shi ya shirya yadda aka hana su Akande tazarce
Osun - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce sharri da kutungwilar Olusegun Obasanjo ne suka ci Bisi Akande a lokacin da yake gwamna a 2003.
Da yake bayani wajen kaddamar da littafin tarihin rayuwar Bisi Akande, shugaban kasar yace Asiwaju Bola Tinubu kadai ya tsira a duk gwamnonin AD.
A zaben 1999, jam’iyyar AD ce ta lashe jihohin kudu maso yamma. Amma zuwa 2003, Olusegun Obasanjo da jam’iyyarsa sun karya jam’iyyar hamayyar.
Punch ta rahoto Muhammadu Buhari ya na tuno yadda gwamnonin AD duk suka gaza samun tazar
ce, illa Bola Tinubu wanda yake mulkin Legas a lokacin.
PDP ta rusa kowa, Tinubu bai tabu ba - Buhari
“Sanannen abu ne kaddara ce ta hau kan Akande – da sauran gwamnonin AD – a wata kutungwila da ta kawo karshen zamansa a kujerar gwamna.”
“Asiwaju Bola Tinubu ne kadai ya tsaya tsayin-daka, ya kubuta daga harin da shugaban kasa (na lokacin), Olusegun Obasanjo ya shirya.” – Shugaba Buhari.
Na san Obasanjo bai da amana - Bisi Akande
Jaridar Daily Trust ta kuma rahoto Cif Bisi Akande yana sukar Olusegun Obasanjo a littafin na sa.
Tsohon gwamnan na Osun ya yi bayani a game da kisan babban ‘dan siyasar Yarbawa a lokacin, Bola Ige, wanda yace mutuwarsa a wancan lokaci ta gigita su.
“Mun zama kamar dabbobi ne babu mai kiwo. AD ta rasa jagoranta, mu ka zama tamkar jirgi ya na yawo a ruwa, ga kifaye za su hadiye mu.” – Bisi Akande.
Cif Akande ya dauko dogon tarihi, tun daga haduwar Obasanjo da Bola Ige a 1960s, da yadda Abacha ya garkame su, zuwa zaben 1999, da zaman Ige Minista.
Akande yace Obasanjo ya roki Ige ya zama Minista a gwamnatinsa, wanda a karshe ya rasa ransa. Akande yace ya san Obasanjo bai da amana, ba abin yarda ba ne.
Littafin tarihin rayuwar Akade
A ranar Alhamis aka ji shugaban kasa ya kwatanta tsohon shugaban jam’iyyar APC na rikon kwarya, Bisi Akande, a matsayin mutum mai gaskiya da amana.
Mai girma Muhammadu Buhari ne ya zama babban bako na musamman a wajen bikin kaddamar da littafin tarihin rayuwar Cif Akande mai suna “My Participation”.
Asali: Legit.ng