Sakataren Gwamnatin Jonathan ya na harin 2023, ya je ya yi kus-kus da IBB da Abdussalami
- Sanata Anyim Pius Anyim ya dage a kan batun neman takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023
- Anyim Pius Anyim ya ziyarci Minna, ya gana da Janar Ibrahim Babangida da Abdulsalami Abubakar
- Tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ya yi magana game da tsarin kama-kama a siyasar Najeriya
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Anyim Pius Anyim, ya kai wa tsofaffin shugaban kasar nan ziyara ta musamman yayin da yake sa rai a kan 2023.
Anyim Pius Anyim ya bayyana cewa ya ziyarci Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Abdulsalami Abubakar kan batun neman takarar da zai shiga.
“Na hadu da tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida da Janar Abdulsalami Abubakar, na yi masu magana a game da niyyar tsayawa ta takarar shugaban kasarmu.”
“Duka shugabannin su na da matukar hangen nesa, kuma sun san kan tarihin kasarmu. Ba su yi mani rowa da shawarwarinsu masu hikima ba.” – Anyim Pius Anyim.
Sanata Anyim Pius Anyim wanda ya taba rike shugaban majalisar dattawa na kasa yace har ya kara jin karfin cewa zai iya neman kujerar shugaban Najeriya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Na sake samun kwarin gwiwar cewa zan iya bada gudumuwa ta wajen cigaban damukaradiyya, a gyara kasar nan, a samu hadin-kai. Ina jin karfin zan iya.” - Anyim.
Jaridar Vanguard ta rahoto ‘dan siyasar ya na cewa mulkin kasar nan ba hakkin wani bangare ba ne kurum, inda yace dole kowa ya na bukatar ‘danuwansa a zabe.
Kamar yadda rahoton ya bayyana, Anyim Pius Anyim ya yi wannan jawabi ne da ya ke magana a wajen wani taro da United For Better Nigeria Initiative ta shirya.
A ra’ayinsa, adalci ne a kyale mutanen yankin Ibo su fito da shugaban kasa a zabe mai zuwa.
Tsohon ‘dan majalisar yake cewa tsarin kama-kama bai cikin tsarin mulkin Najeriya, amma yace idan dai da sanin ya kamata, ya dace Ibo ya zama shugaban kasa.
A dalilin rikicin cikin gida, an ji tsohon mataimakin shugaban majalisar wakilai ya zargi APC da yin murdiya a zaben gwamnan Osun wanda aka yi a shekarar 2018.
Lasun Yusuff yace irinsu Omo-Agege aka yi amfani da su domin a hana shi nasara a zaben 2018.
Asali: Legit.ng