Yadda Buhari ya yi wa Jonathan da PDP adawa a kan cire tallafin fetur kafin ya hau mulki

Yadda Buhari ya yi wa Jonathan da PDP adawa a kan cire tallafin fetur kafin ya hau mulki

  • A shekarun baya Janar Muhammadu Buhari ya na cikin masu yaki a kan janye tallafin man fetur
  • Har a lokacin da yake mulkin soja, Buhari ya ki amincewa ya cire tallafin da ake biya a litar fetur
  • Amma bayan hawan sa mulki a 2015, Buhari ya koma goyon bayan cire tallafi da kara kudin mai

Abuja - Nan da watan Yunin shekarar 2022 ake sa ran cewa gwamnatin tarayya a karkashin Muhammadu Buhari za ta janye tallafin man fetur a Najeriya.

A wajen wani taro da bankin Duniya ya shirya, Ministar kudi, tsare-tsare da kasafin tattalin arziki, Zainab Ahmed, ta ce za a daina biyan tallafin man fetur.

Sai dai Daily Trust ta tuna da baya, a lokacin da mai girma Muhammadu Buhari ya nuna sam bai goyi bayan gwamnati ta janye tallafin da ta ke biya na fetur ba.

Kara karanta wannan

Muna goyon bayan kara farashin man fetur dari bisa dari, Yan kasuwan Mai IPMAN

Wannan matsaya da gwamnati ta dauka, ya ci karo da ra’ayin Buhari kafin ya hau kan mulki.

Buhari sun yi zanga-zanga a kan farashin fetur

Shekaru goma da suka wuce da shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi yunkurin kara farashin fetur, Muhammadu Buhari ya na cikin wadanda suka soke shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idan za a tuna, Daily Trust tace Muhammadu Buhari yace wannan layi da gwamnatin PDP a lokacin ta dauka bai kwanta a ran mafi yawan al’ummar kasar ba.

Buhari ya yi wa Jonathan da PDP
Buhari bai goyon bayan tallafin mai Hoto: Weekly Trust
Asali: UGC

Marigayi Yinka Odumakin wanda yake magana da yawun bakin Buhari a lokacin, ya yi kaca-kaca da wannan shiri, yace da gan-gan aka kashe matatun mai.

Buhari ya yi amai, ya lashe?

Daga baya Buhari ya lashe amansa, yace sam bai taba goyon bayan tallafin mai ba, yace abin da yake yaka shi ne satar kudin da ake yi da sunan an shigo da mai.

Kara karanta wannan

Cire tallafin mai da biyan N5,000: Sai ka rasa wanda ke ba Gwamnatin nan shawara, Dr Ahmed Adamu

A matsayinsa na maras goyon bayan rashin gaskiya, Muhammadu Buhari yace ba zai taba na'am da satar kudin al’umma don kurum a kara farashin litar fetur ba.

Haka zalika a wata hira da aka yi da shi a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa, Buhari yace bai yarda gwamnatin Najeriya ta na biyan wasu kudi da nufin tallafi ba.

Tsohon Ministan man (kuma Minista mai-ci a yau) ya saki wannan layi bayan ya hau mulki, ya na ta yunkurin janye tallafi, ya kara farashin mai kusan sau uku.

An hana jirage 91 tashi

Kun ji cewa shugaban hukumar kwastam na kasa, Hameed Ali (mai ritaya) zai sa kafar wando daya da wadanda suka ki biyan kudin shigo da jiragen samansu.

Kwastam mai yaki da fasa kauri ta umarci hukumomin NCAA, FAAN da NAMA su hana jiragen saman wadannan mutane da ake bi bashi, barin kasa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Minista tayi karin-haske kan yadda za a biya talakawa N5000 bayan cire tallafin mai a 2022

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng