2023: Magoya bayan Osinbajo sun huro wuta, sun ce shi ya kamata ya karbi shugabanci

2023: Magoya bayan Osinbajo sun huro wuta, sun ce shi ya kamata ya karbi shugabanci

  • Wata Kungiya ta fito, ta na taya Farfesa Yemi Osinbajo kamfe domin ya zama Shugaban Najeriya
  • Progressive Consolidated Group ta roki Mataimakin shugaban kasar ya tsaya takara a zaben 2023
  • Mai magana da yawun bakin kungiyar PCG, Barista Emmanuel Pippain yace Osinbajo ya cancanta

Abuja - Da zarar wa’adin Muhammadu Buhari ya cika, sai mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo ya karbi mulki. Wannan shi ne ra’ayin wata kungiya a APC.

Daily Trust ta rahoto cewa wata kungiya ta magoya bayan jam’iyyar APC, ta na so Farfesa Yemi Osinbajo ya samu damar cigaba da ayyukan gwamnati mai-ci.

A ranar Laraba, 24 ga watan Nuwamba, 2021, sakataren yada labarai na kungiyar Progressive Consolidated Group, Emmanuel Pippain ya bayyana wannan.

Kara karanta wannan

2023: Abin da zai hana mu lashe zaben Shugaban kasa da Gwamnonin jihohi inji Jigon PDP

Barista Emmanuel Pippain a madadin kungiyar PCG yace Yemi Osinbajo zai taimaki kasar nan.

Jaridar Independent ta rahoto Pippain yana cewa Farfesa Osinbajo ya dace da rike shugabancin Najeriya, saboda ya san manufofin da kalubalen da ake kai.

Osinbajo
Farfesa Osinbajo a fadar Shugaban kasa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Yakin zama Shugaban kasa a zaben 2023

Kungiyar Progressive Consolidated Group ta bakin Barista Pippain ta roki Yemi Osinbajo ya fito takara, domin ya dare kujerar shugaban kasa a shekarar 2023.

“Kiris ta rage masa ya hau kujerar shugaban kasa, kuma akwai mutane barkatai ‘ya ‘yan APC da ma wadanda babu ruwansu da siyasa, da suke so Yemi Osinbajo ya gaji shugaba Muhammmadu Buhari, saboda taimakon kasa.”
“Mun gamsu cewa Osinbajo ya fi kowa sanin manufofi, nasarori da kalubalen da shugaba Buhari ya fuskanta.”

Kara karanta wannan

Najeriya ba za ta iya juran azabtarwar APC na karin shekaru hudu ba, inji PDP

“Wannan zai bada dama idan APC ta sake kafa gwamnati, ta shiga aiki a shekarar 2023.” – Pippain.

A jawabin na sa Pippain yace PCG da sauran kungiyoyin magoya-bayan Osinbajo za su taru, su dunkule domin su cin ma nasarar manufar da suka sa a gaba.

Sabanin Gambari da Amaechi a Aso Villa

An ji cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ya zargi Ministan sufuri, Rotimi Amaechi da saba doka wajen bada kwangilar ICTN.

Rotimi Amaechi ya maida martani, yana cewa Hadimin shugaban kasar yana neman na sa kason ne a wannan kwangila, har diyar Gambari ta same shi a kan batun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng