Majalisa ta kawo dabarar hana magudin zabe, za a rika aiki da na’ura wajen tattara kuri’u
- 'Yan Majalisar Tarayya sun kammala aikin gyara dokar zabe bayan tsawon lokaci ana kwaskwarima.
- Bakin Sanatoci da ‘Yan Majalisar Wakilai ya zo daya a kan yadda za a rika shirya zaben fitar da gwani.
Babafemi Ojudu yace sai da mataimakin shugaban kasa ya sa baki sannan aka iya cin ma matsaya.
FCT, Abuja - A ranar Talata, 9 ga watan Nuwamba, 2021, kwamitin majalisar dattawa ya kammala aiki a kan yi wa dokar zabe garambawul a Najeriya.
Jaridar Daily Trust tace Sanatoci sun amince da gyare-gyaren da aka yi bayan shugaban masu rinjaye, Yahaya Abdullahi ya tado maganar a majalisa.
Tun a watan Yuli ne majalisar wakilai da sanatoci suka yi aiki a kan dokar zabe ta kasa, inda suka yi wasu kwaskwarima game da zaben fitar da gwani.
‘Yan majalisar dattawa sun bar kofa a bude wajen fito da ‘dan takara, yayin da majalisar wakilan tarayya ta wajabtawa jam’iyyu zaben kato-bayan-kato.
Wannan karo bakin duka ‘yan majalisun ya hadu, inda suka hadu a kan cewa dole ne a yi amfani da tsarin kato-bayan-kato a zabukan tsaida 'dan takara.
Kudirin da Sanatocin suka kawo ya kuma ba hukumar INEC damar ta zabi yadda za ta tattara kuri’u. Za a iya amfani da na’urori domin a inganta zabe.
Yanzu abin da ya rage shi ne a kai kudirin gaban shugaban kasa domin ya rattaba hannu, ya zama doka.
Rawar da fadar shugaban kasa ta taka
Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin siyasa, Sanata Babafemi Ojudu, yace an kai ruwa rana domin a cin ma wannan matsaya a majalisar kasar.
Da yake bayani a shafinsa na Facebook, Babafemi Ojudu yace sai da mataimakin shugaban kasa ya shiga cikin maganar, sannan aka iya samun matsaya.
Wasu suna ganin tsarin zaben fitar da gwanin da kowane ‘dan jam’iyya zai iya kada kuri’a zai gyara siyasa, ta hanyar rage magudin da masu iko suke yi.
Sanatan Kebbi, Mohammed Adamu Aliero yace majalisar Najeriya ta taimaka da ta dauki wannan mataki.
Paris Club: AGF vs Gwamnoni
Da alamu za a ja daga yayin da AGF ya cire wasu kudi daga kason jihohi, ya biya masu bada shawara. An ji cewa wadannan kudi sun kai Naira Biliyan 170.
Kungiyar Gwamnonin Najeriya tace sam ba za ta yarda da wannan aikin da Abubakar Malami ya yi ba. NGF tace Ministan ya saba dokar kasa, kuma ya yi garaje.
Asali: Legit.ng