Zaben Anambra: Mala Buni, Peter Obi, Uzodinma da manyan mutane 4 da APGA ta tonawa asiri
- Jam’iyyar APGA ta sake lashe zaben jihar Anambra, za ta cigaba da mulkar jihar har nan da 2025.
- Baya ga ‘Yan takara 18 da Charles Soludo ya doke, akwai ‘yan siyasan da suka ji kunya a zaben.
- Abin da ya kara ba mutane mamaki shi ne yadda Soludo ya doke Ozigbo har a kauyen Peter Obi.
Anambra - Jam’iyyar All Progressive Grand Alliance watau APGA ce tayi nasara a zaben sabon gwamnan jihar Anambra, ta doke jam’iyyu har 18.
Jaridar Daily Trust ta kawo jerin wasu ‘yan siyasa da suka sha kashi a zaben. Wadannan mutane su ne nasarar Chukwuma Soludo za ta fi yi wa ciwo.
1. Nkem Okeke
Nkem Okeke shi ne mataimakin gwamna Willie Obiano a karkashin APGA. Daf da zabe ya sauya-sheka zuwa APC, amma bai iya tsinana mata komai ba.
2. Peter Obi
An yi mamakin yadda Peter Obi wanda ya yi takarar mataimakin shugaban kasa a PDP a 2019 ya gaza tabuka wani abu a zaben duk da ya yi gwamnan jihar.
3. Mai Mala Buni
Zaben Anambra bai yi wa shugaban rikon kwarya na APC, Mai Mala Buni dadi ba. Buni ya sa ran APC za ta karbe Anambra kamar yadda ta fara mamaye yankin.
4. Hope Uzodinma
Za a ga laifin gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma a rashin nasarar Andy Uba. Uzodinma shi ne kusan jagoran jam’iyyar APC a yankin na kudu maso gabas.
5. Bianca Ojukwu
Bianca Ojukwu wanda ta yi Chukwuemeka Odumegwu takaba ta ji kunya a wannan zabe. Bianca ta samu sabani da jagororin APGA gabanin zaben gwamnan.
6. Stella Oduah
Wata mace da Daily Trust ta kawo a jerin na ta ita ce Sanata Stella Oduah wanda ta sauya-sheka zuwa APC. Uba ya sa rai tsohuwar Ministar ta taimaka masa.
7. Chukwuma Umeoji
Honarabul Chukwuma Umeoji mai wakiltar mazabar Aguata a majalisar wakilai ya ji kunya a zaben bayan rikicin tikiti da ya yi tayi da Charles Soludo a kotu.
Fadan Buhari da Ahmad Gumi
Ashe tun bayan zaben 2007, shugaban kasa Muhammadu Buhari yake rike Ahmad Gumi a rai, saboda ya bada shawarar ka da a shigar da Umaru 'Yar'adua kotu.
Tukur Mamu yace Gumi ya kara batawa Buhari rai a 2015, lokacin da ya bada shawarar shi da Goodluck Jonathan duk su hakura da shiga zaben shugaban kasa.
Asali: Legit.ng