Zaben Anambra: Bayani a kan ‘Dan takarar APC wanda ya taba yin Gwamna na kwana 17
- Emmanuel Nnamdi Uba shi ne ke rike da tutar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Anambra.
- Sanata Andy Uba kamar yadda aka fi sanin shi, ya yi suna a Najeriya tun da ya shiga siyasa a 1999.
- Uba ya taba zama Hadimin shugaban kasa, kuma ya yi ‘yan kwanaki a kan kujerar gwamna a 2007.
Anambra- Daya daga cikin ‘yan takarar da za a gwabza da su a zaben gwamnan jihar Anambra shi ne Emmanuel Nnamdi Uba wanda aka fi sani da Andy Uba.
Sanata Andy Uba yana cikin gawurtattun kusoshin jam’iyyar PDP a gwamnatocin baya. Yanzu haka shi ne ke rike da tutar APC a zaben da za ayi ranar Asabar.
Andy Uba ya dawo Najeriya ne bayan Olusegun Obasanjo ya zama shugaban kasa. A lokacin da yake Ingila, Uba ya taimakawa Obasanjo a zaben shekarar 1999.
Fitaccen 'dan siyasar mai shekara 62 ya taba lashe zaben gwamna da na sanata a jihar Anambra, amma duk bai dade sosai a kan karagar mulki ba, kotu ta tsige shi.
Legit.ng ta tattaro maku muhimman abubuwa da kuke bukatar sani a game da rayuwar Andy Uba:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
1. Lashe zaben Gwamna a shekarar 2007
Andy Uba ya yi takarar gwamnan Anambra a karkashin PDP a 2007, kuma ya lashe zabe. Kwanansa 17 a kujera sai kotun koli ta dawo da Peter Obi kan mulki.
2. Na hannun-daman Obasanjo a Aso Villa
Sanata Andy Uba yana cikin manyan na-kusa da Olusegun Obasanjo a lokacin da yake shugaban kasa. Uba shi ne mai kula da harkokin shugaban kasar na cikin-gida.
3. Ya ga samu ya ga rashi a kujerar Sanata a 2012
Uba ya shiga takarar Sanata a 2011, kuma ya doke Chukwmaeze Nzeribe na APGA. Daga baya kotu tace a sake zabe a 2012, Sanata Ikechukwu Obiorah ya yi nasara
4. Attajirin 'Dan siyasa yana auren Fasto
Babban ‘dan siyasar yana auren Fasto Faith Vedelago wanda ta haifa masa yara biyu. Mai dakin ta sa ce shugabar cocin Faith Miracle Center da ke birnin tarayya, Abuja.
Rotimi Amaechi zai yi takara a 2023?
Idan mu ka koma batun zaben 2023, an ji Tonye Princewill ya fito yana cewa Rotimi Amaechi ya cancanta ya zama Shugaban kasa kamar yadda wata kungiya ta fada.
Princewill yace Amaechi ya yi shugaban majalisar dokoki a Ribas, ya yi Gwamna na shekaru takwas, har ya zama Shugaban Gwamnoni kafin a nada shi Minista.
Asali: Legit.ng