2023: Kungiyar Yarbawa ta tsaida ‘Dan takararta tilo a zaben Shugaban kasa daga APC
- Yoruba Welfare Group ta bayyana zabin ta a zabe mai zuwa na 2023
- Kungiyar tana goyon bayan Bola Tinubu ne ya karbi mulkin Najeriya
- Wannan sanarwa ya fito ta bakin shugaban YWG, Adegoke Alawuje
Oyo - Wata kungiyar Yarbawa mai suna Yoruba Welfare Group tace ta amince da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin ‘dan takararta a zaben 2023.
Jaridar Daily Trust ta fitar da wannan rahoto a ranar Talata, 26 ga watan Oktoba, 2021.
Yoruba Welfare Group ta yi kira ga sauran jam’iyyun siyasan Najeriya da za su shiga takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa, su bi irin layinsu.
Wannan kungiya ta nuna farin cikin ta a game da irin soyayya, kauna, da hadin-kan da ake samu tsakanin ‘yan siyasan Kudu maso yammacin Najeriya.
A cewar wannan kungiya da ta kan tsoma baki a siyasa idan ta kama, sabanin fahimta da bambancin ra’ayin siyasa bai raba kan manyan Yarbawa ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kwamred Adegoke Alawuje ya fitar da jawabi
Jawabin kungiyar ya fito ne ta bakin hadimin shugaban ta na kasa, Elder Yinka Salaam a madadin shugaban, Kwamred Adegoke Alawuje a jiya.
Kwamred Adegoke Alawuje yace daukacin shugabannin Yoruba Welfare Group na fadin Duniya, sun amince da Bola Tinubu a matsayin zabin na su.
Alawuje ya yi kira ga mutanen Najeriya su mara masu baya, sannan su daina sauraron surutan da ake yi a game da halin rashin tsaro da ake fama da shi.
Ana kukan Boko Haram da ‘yan bindiga a Arewa ta gabas da kuma Arewa ta yamma, haka zalika ‘yan ta’addan IPOB sun addabi jihohin kudu maso gabas.
Shugaban YWG na kasa ya yi kira ga ‘yan siyasan Yarbawa su maida hankali wajen bunkasa tattalin arzikin yankin ta yadda matasa za su samu abin yi.
Rashin tabbas a PDP
Ku na da labari cewa ana saura kwanaki ayi zaben PDP, tsohon shugaban jam’iyya, Prince Uche Secondus ya na shirin kawo matsala da karar da ya kai.
Kwanan nan shugabannin PDP za su san ko za a iya shirya zabukan shugabanni na kasa idan kotu ta yanke hukunci a kan karar da Secondus ya shigar.
Asali: Legit.ng