Wike ya yi kaca-kaca da mulkin Buhari, yace abubuwa ba su taba tabarbarewa haka ba
- Nyesom Wike yace Gwamnatin Tarayya ta kawo sabon salon kassara ‘Yan adawa
- Gwamnan na PDP ya yi kaca-kaca da Muhammadu Buhari a taron kungiyar NBA
- Wike ya zargi Gwamnati da gaza tsare jama’a, da kuma tauye hakkin zanga-zanga
Rivers – Mai girma Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yace ba a taba yin lokacin da Najeriya ta ke fama da matsalar jagoranci kamar wannan lokaci ba.
Punch ta rahoto Nyesom Wike yana wannan jawabi ne a ranar Litinin, 25 ga watan Oktoba, 2021.
Gwamna Nyesom Wike ya zargi gwamnatin tarayya da kassara ‘ya ‘yan jam’iyyar hamayya, yace ana yi masu sharrin cewa sun zama barazana ta fuskar tsaro.
Nyesom Wike yace bayan an yi wa ‘yan adawar wannan cinne, sai kuma a karbe masu fasfon waje.
Gwamnan na Ribas ya yi wannan jawabi ne a wajen taron kungiyar lauyoyi na kasa watau NBA na shekara-shekara, wanda aka bude na bana a garin Fatakwal.
Wike ya zargi gwamnatin tarayya da Muhammadu Buhari yake jagoranta da jefa al’umma a matsin lamba, da gaza tsare rayuka cikin tsawon shekaru shida.
Abin da Nyesom Wike ya fada a taron NBA
“Ba a taba yin wani lokaci a tarihin Najeriya da aka yi mulki maras kan gado irin yanzu ba."
“Gwamnatin tarayya ta gaza sauke nauyin samar da tsaro ga jama’a kamar yadda muke gani a shekaru shidan nan da suka wuce.” - Wike
A cewar Nyesom Wike, duk ranar Duniya ana kara tauye hakkin mutane na yin zanga-zangar lumuna, yace gwamnati ta na buga mulkin kama-karya.
Babu wanda ya tsira - Wike
“An shiga hakkin Bayin Allah ta yadda har Alkalan manyan kotu, har da na kotun koli ba su tsira ba. Ana shiga gidansu cikin dare, ana kai masu farmaki.”
“Yanzu abin da aka shigo da shi, shi ne a yi wa mutane da ba su da laifi da ‘yan adawa sharri, sai a karbe masu fasfo, ba tare da umarnin kotu ba.” – Wike.
EFCC tana binciken Anyim Pius Anyim
A farkon makon nan ne labari ya zo cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Anyim Pius Anyim ya shafe awa da awanni a ofishin EFCC, yana shan tambayoyi.
Ana zargin Tsohon shugaban majalisa da tafka badakala a Gwamnatin Jonathan. Lambarsa ta fito yayin da ake binciken kudin da aka wawura a ma'aikatar jiragen sama.
Asali: Legit.ng