APC tana da mabiya miliyan 40, za ta lashe zaben 2023 a cikin sauki inji Sakataren APC na kasa

APC tana da mabiya miliyan 40, za ta lashe zaben 2023 a cikin sauki inji Sakataren APC na kasa

  • John Akpanudoedehe yace jam’iyyar APC tana da mabiya miliyan 40 a Najeriya
  • Sanata Akpanudoedehe yake cewa wannan ne zai ba APC damar lashe zaben 2023
  • Sakataren na APC ya sha alawashin yin nasara a zabukan Ekiti, Osun da Anambra

Abuja - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tace za ta yi galaba da kyau a zabukan gwamnonin jihohin da za ayi a Anambra, Osun da Ekiti.

Jaridar Premium Times ra rahoto sakataren jam’iyyar APC na rikon kwarya, Sanata John Akpanudoedehe yana cewa suna da mabiya miliyan 40.

John Akpanudoedehe ya bayyana wannan ne a lokacin da yake kadammar da kwamitocin da za su saurari korafai a zabukan da APC ta gudanar a jihohi.

An rahoto Akpanudoedehe yana cewa a cikin sauki jam’iyyar APC za ta lashe zabe, saboda adadin mabiyanta.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke a jam'iyya bayan dakatar da shugabanta da sakatarensa

Sakataren jam’iyyar na riko yake cewa akwai kokarin da APC ta ke yi na ganin ta kara karfi, sannan ta kafa gwamnatoci a Anambra, Osun da Ekiti.

Sakataren APC na riko
Sanata John James Akpanudoedehe Hoto: von.gov.ng
Asali: UGC

Mutum miliyan 40 suka yi rajista da APC - Akpanudoedehe

“Da adadin dinbin mabiyanmu da suka yi rajista, babu shakka mutanen Najeriya sun yadda da mu, kuma za mu lashe zabukan da za a yi.” – Akpanudoedehe.
"Fara wa da zabukan Anambra, zuwa Osun, da Ekiti dakuma babban zaben 2023.”

Akpanudoedehe yace al’umma sun fahimci Muhammadu Buhari yana da niyyar alheri, kuma zai yi bakin kokarinsa wajen samar da abubuwan more rayuwa.

Sakataren na APC yace dole a hada-kai domin yakar wadanda suka sha alwashin ruguza kasa, ya kawo misali da kai hari a filin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Kara karanta wannan

Sai mun hada kai ne za mu iya cin galaba a kan miyagu – APC kan harin jirgin kasa

A karshe, Akoanudoedehe ya yi kira ga ‘yan kwamitin da aka kafa da su yi adalci, su saurari korafi daga kowane bangare yayin da ake fama da rigingimu.

Rarara yana so Buhari ya kai 2028

Dauda Adamu Kahutu Rarara ya bayyana cewa zai so Muhammadu Buhari ya yi ta mulki har 2028, yace tun yana yaro ake cewa Buhari yana da gaskiya, har yau.

Rarara ya rangadawa Shugaban Najeriya Buhari wakoki 66 saboda kawai yana da gaskiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng