Daram-dam-dam: Osinbajo bai hakura da neman Shugaban kasa a 2023 ba inji Kungiya
- The Progressive Consolidation Group ba ta cire rai da takarar Yemi Osinbajo ba
- Kungiyar magoya bayan ta musanya rade-radin cewa Osinbajo ya janye takara
- Shugaban PCG yace Osinbajo bai tsaida magana game da shiga zabe a 2023 ba
Abuja - Wata kungiya mai suna The Progressive Consolidation Group, tace tana kokarin ganin Yemi Osinbajo ya zama shugaban kasa a zaben 2023.
Wannan kungiya ta magoya bayan mataimakin shugaban kasar ta fito tana musanya batun cewa Osinbajo ya hakura da neman takarar shugaban kasa.
Punch ta rahoto PCG tana cewa aikin da ke gaban Farfesa Osinbajo a yanzu shi ne maida hankali kan nauyin da ke gabansa na mataimakin shugaban kasa.
Shugaban wannan kungiya yake cewa rashin nacin Yemi Osinbajo na ganin ya zama shugaban kasa, ya sake karasa masa karbuwa wajen magoya baya.
Kamar yadda muka samu rahoto, Dr. Aliyu Kurfi ya yi wannan jawabi ne a ranar 24 ga watan Oktoba, 2021, a babban birnin tarayya da ke garin Abuja.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
‘2023: Mun kara yin amanna da Osinbajo-Kungiya’
A jiya Aliyu Kurfi ya fitar da jawabi da ya yi wa take da; ‘2023: Job focus and non-desperation further reinforces supporters’ confidence in Osinbajo-Group.’
“Mataimakin shugaban kasarmu, Yemi Osinbajo (SAN), yana cikakkiyar biyayya ga mai gidansa, shugaban kasa Muhammadu Buhari.”
“Ya maida hankali sosai kan aikinsa, kuma ba a taba yi masa shaida da buri ya rufe masa ido ba.” - Aliyu Kurfi
Farfesa Yemi Osinbajo bai janye wa kowa ba
“Ya zama dole a fito a karyata cewa Osinbajo ya halarci wani taro, inda ya yi fatali da burinsa na neman shugaban kasa a 2023, ko ya janyewa wani ‘dan siyasa.”
“Tsantsagwaron karya ne, ya za ayi ya hakura a lokacin da bai karbi tayi ko ya yi watsi da shi ba?”
Jaridar Premium Times tace PCG tace wasu ne suke ta kawo kanzon kuregensu, a karshe tace ba za ta yarda da siyasar jagaliya a tafiyar jam'iyyar APC ba.
Ra'ayin MURIC a kan zaben 2023
Dazu kungiyar nan mai kare hakkin musulunci, MURIC tace babu Musulmin Bayaraben da ya taba zama Shugaban kasa ko Mataimaki a tarihin Najeriya.
Shugaban MURIC ya kawo Musulman kasar Yarbawa da suka cancanta da mulkin kasar nan. Daga cikin su akwai Bola Ahmed Tinubu da Rauf Aregbesola.
Asali: Legit.ng