El-Rufai, Ganduje, Yahaya Bello da Gwamnoni 4 da suka halarci Jami’ar Ahmadu Bello

El-Rufai, Ganduje, Yahaya Bello da Gwamnoni 4 da suka halarci Jami’ar Ahmadu Bello

  • Jami’ar Ahmadu Bello ta yi fice wajen yaye fitattun mutane a fadin Duniya
  • Yanzu haka akwai wasu Gwamnoni masu ci da a jami’ar suka yi karatunsu
  • Daga cikin Gwamnonin akwai MNasir El-Rufai da Abdullahi Umar Ganduje

Zaria - Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria ta yaye daliban da suka zama manya a Najeriya. Daga ciki har da shugaban kasa, gwamnoni da Ministoci.

TheAbusites.com ta tattaro jerin daliban jami’ar da suka zama gwamnoni a kasar nan. Tsakanin shekarar 1999 da 2007, jami’ar ta fito da gwamnoni 37.

Yanzu haka akwai gwamnoni bakwai da ke ofis wadanda duk sun halarci wannan babbar makaranta.

Gwamnonin da suka yi karatu a ABU Zaria

Ga su nan kamar yadda TheAbusites.com ta jero su:

Kara karanta wannan

An hurowa Buni wuta ya hukunta Shekarau, Aregbesola, ya koyawa manyan APC hankali

1. Darius Dickson Ishaku

Gwamnan jihar Taraba, Darius Dickson Ishaku ya karanta ilmin zane a jami’ar ABU Zaria. Ishaku ya yi digirgir a jami’ar a bangaren tsare-tsaren birane.

2. Simon Bako Lalong

A shekarar 1999 ne gwamnan Filato, Simon Lalong ya gama digiri a bangaren shari’a a jami’ar ta ABU Zaria. Daga baya ya yi digirgi a jami’ar UNIJOS.

3. Yahaya Adoza Bello

A 1999 da 2002 gwamna Yahaya Adoza Bello ya samu shaidar digiri da digirgir a fannin ilmin akawu da kasuwanci, duk a wannan jami’a mai tarihi.

El-Rufai, Ganduje, Yahaya Bello da sauran su
Gwamnonin da suka je ABU Zaria Hoto: www.theabusites.comwww.theabusites.com
Asali: UGC

4. Abdullahi Umar Ganduje

Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi digiri a ilmin karantarwa a jami’ar Ahmadu Bello a 1975. Daga baya ya je gwamnan na Kano ya tafi wasu jami’o’in.

5. Nasir Ahmad El-Rufai

Malam Nasir Ahmad El-Rufai yana cikin gwamnonin da suka halarci wannan jami’a. Tsohon Ministan na Abuja yayi digiri a fannin zane-zane.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta dauki nauyin Daliban Chibok 57, sun fara karatun Digiri a Jami’ar Atiku

6. Mohammed Badaru Abubakar

Gwamna Mohammed Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya yi digirinsa ne a jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. Badaru ya karanta ilmin akawu a jami’ar.

7. Muhammad Inuwa Yahaya

Kamar gwamnan Jigawa, Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya na digiri a harkar akawu duk a wannan jami’a, ya kammala karatunsa a 1983.

8. Samuel Ioraer Ortom

A shekarar 1995 Samuel Ioraer Ortom ya samu shaidar IJMB a jami’ar ABU Zaria. Bayan shekaru uku ya kammala karatun difloma a ilmin aikin jarida.

Rabiu Kwankwaso ya kafa tarihi

A baya kun ji cewa da yake bikin cika shekara 65, tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso ya kaddamar da wani asibitin duba masu yin shaye-shaye.

Wannan asibitin zai taimaka wa duk ‘yan shaye-shayen da suke kokarin gyara halinsu. Wannan asibiti na musamman shi ne na farko da wani ya kafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng