
Siyasa







Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya ce Sanata Rabiu Kwankwaso zai dawo APC saboda NNPP ta mutu murus a Najeriya. Ganduje ya ce masu shirin hadaka za su wargaje.

Sanatan da ke wakiltar Jigawa ta Arewa maso Gabas, Sanata Abdul Hamid Malamadori, ya nuna goyon bayansa ga takarar Gwamna Umar Namadi a zaben 2027.

Gwamnan jihar Akwa Ibom na jam'iyyar PDP, Umo Eno, ya bayyana matsayarsa kan takarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027. Ya nuna goyon bayansa ga Tinubu.

Jam’iyyar PDP a Ondo ta koka kan matsaloli inda ta yi barazanar neman dokar ta-baci idan Gwamna Aiyedatiwa ya kasa magance matsalar tsaro ba da ke addabar al'umma.

A yayin da ake tunkarar zaben 2027, APC reshen jihar Borno ta amince da tazarcen Shugaba Bola Tinubu tare da neman ya sake rike Shettima matsayin mataimakinsa.

Shugabannin APC a Kano ta Kudu sun fara zawarcin Sanata Kawu Sumaila ya fita daga NNPP zuwa APC yayin da ake cigaba da samun sabani tsakanin shi da Kwankwaso.

Yayin da ake tunkarar zaben shugaban kasa, rigima ta barke tsakanin ɗan Atiku Abubakar da ɗan gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, kan batun takarar shugaban ƙasa a 2027.

Wata kungiyar matasa ta bayyana cewa za ta hada kan mutane miliyan 5 domin nuna jin dadin mulkin Bola Tinubu a jihar Abia tare da goyon bayan Sanata Orji Kalu.

Shugaban gwamnonin PDP, Bala Mohammed ya bayyana cewa suna yiwa tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar, Atiku Abubakar fatan alheri da hadakar jam'iyyunsa.
Siyasa
Samu kari