Abin da ya sa aka ji na ba Fati Slow kyautar N1, 000, 000 Inji Naziru Sarkin Waka
- Naziru M. Ahmed ya ba shahararriyar ‘yar wasar kwaikwayo a Kannywood, Fati Usman kyauta
- Fitaccen mawakin ya ba Tauraruwar da aka fi sani da Fati Slow kyautar kudi, Naira miliyan daya
- Mawakin ya ce wani hadisin Manzon Allah SAW ya tuna, hakan ta zaburar da shi wajen yin alherin
Kano - Kwanakin baya aka ji shahararren mawaki kuma ‘dan wasan nan, Naziru M. Ahmed ya yi wata kyautar da ta ba yawan al’umma mamaki.
A wata hira ta musamman da Tambarin Hausa TV ta yi da Naziru M. Ahmed, an nemi a ji daga bakinsa, abin da ya sa ya ba Fati Slo kyautar kudi.
Kamar yadda za a ji a wannan hira, Alhaji Naziru Ahmed wanda aka fi sani da Sarkin Waka ya bayyana dalilin da ya sa ya maida sharri da alheri.
Fitaccen mawakin yake cewa ya tashi daga barci sai ya ji ana ta magana a game da kalaman da Fati Slo tayi, har ana ba shi shawarar ya kai kara.
Mawakin ya bayyana cewa abokansa da suke aikin lauya sun yi masa maganar cewa a shiga kotu. An wallafa bidiyon hirar a shafin Facebook.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hadisin Annabi (SAW)
A nan ne sai ya ce wani hadisin Manzon Allah Muhammad (SAW), ya bijiro masa, wanda da shi ya yi amfani, ya ba jarumar wasan kwaikwayon kyauta.
Gundarin wannan hadisi na Annabi SAW yana cewa:
“Ku ji tsoron Allah SWT a duk inda ku ka samu kan ku, ku biyo aikin sharri da na alheri, na alherin zai shafe sharrin, ku mu’amulanci mutane da kyakkyawan dabi'a."
Abu Dharr da Mu’adh Jabal suka ji wannan hadisi daga bakin Annabi SAW. Tirmidhi ya inganta hadisin a littafinsa.
Abin mamaki, bayan Nazir Ahmed ya cika alkawarin da ya yi wa tauraruwar, sai aka ji ta fito fili ta na ba shi hakuri a kan laifin da ta yi masa a baya.
An gayyaci mawakin ne a shirin AmonGaskiya wanda aka saba yi a wannan gidan talabijin.
Martanin mutane a Facebook
Wasu daga cikin wadanda suka saurari hirar a shafin Facebook sun rika yabawa mawakin, su na cewa:
Naziru Sarkin Wwaka. Allah yayi maka albarka ya kara daukaka da juriya da jajircewa wajen fadar gaskiya da kuma neman yadda za'a kawo gyara. Hakika duk me fadin gaskiya dole ya hadu da kalubale daga wadanda basu son gaskiya . San a dawwama akan rashin gaskiya shine yasa babu cigaba a kasa. Allah ya kara mana hakuri da tausayi da tunani mai amfani. Amma kuma ai ba a taru duk anzamo daya ba dan haka bai kamata a hada masu laifi da marasa laifi ace ma'unin su daya ba. Duk inda jamaa take sai ansamu na kirki da wadanda ba na kirki ba. Muyi ta addu'a Allah ya kyautata rayuwarmu mu zama mutanen kirki gaba daya. Amin summa amin.
- Zuhra Abdulhamid Hassan
TABBAS ALHAJI MUHAMMAD NAZIRU SARKIN WAQA BAQARYA UP UP UP NAZIRU SARKIN WAQA KAF KANNYWOOD BABU KAMAR KA YA ALLAH YA JIQAN MAGABATAN MU
- Ibrahim Danmusa
Tabarar Fati Slow
Kwanaki an ji cewa Fati Usman wanda aka fi sani da Fati Slow ta ba Naziru Sarkin Waka hakuri a kan tabarar da ta yi masa a kafafen sada zumunta.
Tsohuwar jarumar ta Kannywood ta bayyana cewa ‘kebura’ ne suka jawo ta yi abin da ta yi a baya. Hakan ya na nufin halin matsin rayuwa ya addabe ta.
Asali: Legit.ng