Budurwa ta mari saurayinta bainar jama'a saboda ya ki amincewa ya aureta bayan shekaru 6 suna tare

Budurwa ta mari saurayinta bainar jama'a saboda ya ki amincewa ya aureta bayan shekaru 6 suna tare

  • Wata budurwa ta janyo cece-kuce yayinda ta waskawa saurayinta mari a cikin jama'a saboda ya ki amincewa ya aureta
  • A bidiyon da ya yadu a kafafen ra'ayi da sada zumunta, budurwar ta bukaci saurayin ya aureta amma yace ba ya yi
  • Cikin fushi kawai ta maresa saboda ta dade tana rokonsa su yi aure bayan shekaru shida suna soyayya

Wata budurwa ta fusata yayinda saurayin da suka kwashe shekaru suna soyayya ya watsa mata kasa a ido.

A wani faifan bidiyon Youtube da Foreverdope Records ta nada, budurwar na cikin shakatawa da saurayin kawia sai ta tsugunna kasa don bukatar ya aureta.

Budurwa ta mari saurayinta
Budurwa ta mari saurayinta bainar jama'a saboda ya ki amincewa ya aureta bayan shekaru 6 suna tare Hoto: Foreverdope Records a YouTube
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Budurwa mai shekara 22 za ta yi wuff da tsoho mai shekara 76, tace babu gudu ba ja da baya

Da alamun saurayin bai gamsu da hakan ba inda ya fara kokarin tada da ita kuma jama'a sun fara taruwa.

Yayinda ta ki tashi daga kasa, kawai sai yace mata tayi hakuri ba zai aureta ba.

Da alamun hakan bai yi mata dadi ba inda ta mika tsaye ta waskeshi da mar a fuska.

An ruwaito cewa sun kwashe shekaru shida suna soyayya.

Kalli bidiyon:

Yan Najeriya sun tofa albarkatun bakinsu:

Musbahu Bala:

Kai kinyi mistake Aida kinkaishi Kara kutu
Kinga kema da yabiya ki kudin bata lokaci da kuma kudin chizon sauro da na kwalliyar da kikaimasa

Ayeshat Muhammad Ahmad tace:

Shine tayi laifi,, aibata burgeni ba, dabatasa Yan unguwa sun karya matashiba,, azzalumi kawai six years Yana bata mata lokaci

Adamu Zumunta Aliero yace:

Shi aure nufin Allah ne
Amma kuma kin wulakantashi
Shikuma bai kyautaba
Allah takaita wannan masifa tsakinsu

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng