Bidiyon Ƙasaitattun Kayan Alatu Da Matashi Ya Saka a Gidansa Na Kasa, Ciki Har Da AC, Babban TV Da Kujeru

Bidiyon Ƙasaitattun Kayan Alatu Da Matashi Ya Saka a Gidansa Na Kasa, Ciki Har Da AC, Babban TV Da Kujeru

  • Soshiyal midiya ta dauki zafi bayan bayyanar wani bidiyo wanda wani mutum ya nuna kayan alatun da ya zuba a cikin gidansa
  • Mutumin cike da alfahari ya nuna yadda ya kawata cikin gidansa na kasa da tsadaddun kayan amfani har da na’urar sanyaya wuri ta AC
  • Yayin da mutane su ke mamakin irin dukiyar da ya zuba a gidan kasar, wasu kuma sun yi mamakin yadda mai dukiya irinsa ya tsaya cikin gidan kasa

Hausawa su kan ce hangen dala ba shiga birni ba, tabbas batun haka yake bayan bayyanar bidiyon tarin kayan alatun da wani mutum ya zuba wa gidansa na kasa a kafafen sada zumunta.

Kamar yadda ake ganin sauran gine-gine na kasa a kauyuku, haka gidan yake, sai dai idan aka duba cikinsa abin ba a cewa komai don ya hadu iya haduwa.

Kara karanta wannan

Babban Dalilin mu na kin fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci a Najeriya, Malami

Bidiyon Ƙasaitattun Kayan Alatu Da Matashi Ya Saka a Gidansa Na Kasa, Ciki Har Da AC, Babban TV Da Kujeru
Kaya masu tsada da matashi ya zuba a gidan kasa: Hoto: @gossipmilltv
Asali: Instagram

Wani bidiyo wanda gossipmilltv su ka wallafa a shafinsu na Instagram ya janyo cece-kuce iri-iri.

A falon gidan wani mutum na kasa har da na’urar sanyaya wuri ta AC, sannan wasu luntsuma-luntsuman kujeru na kece raina tare da fenti na gani da fadi.

Idan mutum ya duba uwar dakansa da kuma yadda ya jera takalma, huluna har da agogonsa mai kirar Rolex wanda yace N100,000 ya siyo shi sai ya bude baki saboda mamaki.

Ba'a dai a samu cikakken bayani dangane da inda gidan yake ba har yanzu.

Wannan bidiyon ya janyo cece-kuce inda mutane su ka dinga tofa albarkacin bakunansu

Am_mayana27 ta ce:

“Irin rayuwar mazan Ghana kenan.. Za ka gansu a gida mara kyau mai arhar haya amma dakunansu masu bala’in kyau.”

Kara karanta wannan

Ana wata: Shehin malami ya magantu, ya ce mata su daina yiwa mazajensu girki da aikin gida

T.r.ea.sure ta rubuta:

“Ah ahhh? Menene na karya Mr Linus? Ka makala na’urar AC a cikin daki da falo.. Ina fankar AC din da ake ajiyewa ta waje?”

Iretiwalola ta yi tsokaci da:

“Mutanen nan sun zaci mu ‘yan Instagram ba mu da hankali.. idan ka kalli bidiyon ta waje.”

24.007 ta ce:

“Gaskiya gyaran gidan ya yi kyau, amma bai dace wanda zai iya siyan irin wadannan kayan alatun ya zauna a ginin kasa ba, amma ya ban dakin zai kasance?”

Machidalooks ya ce:

“Boye wa EFCC ake yi anan kuma mun gano wannan salon. Ba ku da aiki sai nemo ginin kasa, sai sun gano ku.”

Shugaban wurin aiki ya ba na ƙasa da shi da ke tattaki zuwa wurin aiki kyautar mota

A baya, kun ji wani matashi, Walter, ya yi tattakain mil 20 a ranar sa ta farko ta zuwa wurin aiki. Motar sa ta samu matsala ana gobe zai fara zuwa aikin hakan ya sa ya yanke wannan shawarar.

Kara karanta wannan

Mota ta farko da zan hau ni zan kera ta : Yaron Najeriya da ya hada mota da karafuna

Kafin safiyar, ya yi kokarin tuntubar abokan sa amma babu alamar zai samu tallafi saboda ya sanar da su a kurarren lokaci kamar yadda Understanding Compassion ta ruwaito.

Daga nan ne ya yanke shawarar fara tattaki tun karfe 12am don isa wurin aikin da wuri. Matashin bai bari rashin abin hawan ya dakatar da shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164