Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Lokoja na jihar Kogi, ta sauya janye hukuncin da ta bada na tilastawa hukumar INEC yin rajistar jam'iyyar NDC.
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Lokoja na jihar Kogi, ta sauya janye hukuncin da ta bada na tilastawa hukumar INEC yin rajistar jam'iyyar NDC.
An samu rahoton cewa mutane da ke aiki da Sunday Igboho domin farautar 'yan bindiga sun hadu da fushin 'yan bindiga. An yi wa mutanen Igboho jina-jina.
Abdullahi Umar Ganduje ya dakatar da kafa Hisbah mai zaman kanta a jihar Kano. An dakatar da Hsibar Ganduje ne bayan zama da DSS da 'yan APC a jihar Kano.
An shiga tashin hankali a garin Ora da ke kan iyakar Osun da Kwara bayan ‘yan bindiga sun kashe basarake tare da sace tsohon jami’in Kwastam a wani sabon hari.
Wani jirgin sama na masu kudi da ya taso daga Kaduna ya yi hatsari a filin jirgin Owerri bayan ya samu matsala a sararin samaniya, NSIB ta ce babu asarar rai.
Wasu rahotanni sun yada cewa Hukumar DSS ta cafke malamin addinin Musulunci a jihar Osun bayan yada bidiyonsa yana zanga-zanga kan Falasɗinu amma ya karyata hakan.
Aliko Dangote ya kai ƙara ICPC kan shugaban NMDPRA, Farouk Ahmed, bisa zargin kashe sama da $7m wajen karatun ’ya’yansa a Switzerland. Ya nemi a kama shi.
Sabon littafi da aka ƙaddamar a Abuja ya bayyana cewa Muhammadu Buhari ya amince da sake fasalin Naira ne domin dakile sayen kuri’u, ba don cutar wata jam’iyya ba.
Harin jiragen saman NAF a Kukawa, jihar Borno, ya hallaka fararen hula ciki har da masunta da direbobi, yayin da ake binciken sahihancin bayanan sirri.
Kasar Najeriya na shirin karɓar jiragen yaƙi M-346 guda 24 daga ƙasar Italiya, bayan yarjejeniya da kamfanin tsaro na Leonardo domin yaki da ta'addanci.
Rahotanni sun bayyana cewa mutanen gari sun yi kukan kura sun tare wata dabar yan bindiga, sun kama daya daga ciki kuma sun kashe shi a jihar Zamfara.
Labarai
Samu kari