Hukumar NISO Ta Fitar da Rahoto, Ta Karya Karfin Gwiwar 'Yan Najeriya kan Wutar Lantarki

Hukumar NISO Ta Fitar da Rahoto, Ta Karya Karfin Gwiwar 'Yan Najeriya kan Wutar Lantarki

  • 'Yan Najeriya na ci gaba da fuskantar rashin wadatacciyar wutar lantarki duk da kokarin da gwamnatin kasar ta sha cewa tana yi
  • A wani rahoto da hukumar NISO ta fitar, ta nuna cewa wutar lantarki da ake samarwa a Najeriya ba ta wuce megawatt 4,300 ba
  • Wannan adadin wuta ya nuna gibin megawatt 11,200 idan aka kwatanta da karfin samar da wuta da ake da shi na megawatt 15,500 a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Fatan ‘yan Najeriya na samun wadatacciyar wutar lantarki mai dorewa na ci gaba da zama kamar mafarki yayin da kasar ke ci gaba da samun komawa baya a fannin.

Sabon bayani daga Hukumar Kula da Tsarin Wutar Lantarki ta Najeriya (NISO) ya nuna cewa matsakaiciyar wutar lantarki da ake samarwa a Najeriya bai wuce megawatt 4,300 ba.

Kara karanta wannan

Amurka ta ji wuya: Trump ya cirewa Iran takunkumin man fetur

Lantarki.
Turakun da ke dakon wutar lantarki a Najeriya Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Kira ga ayyana dokar ta-baci

A rahoton da Vanguard ta fitar, wannan dadin wuta ya nuna gibin megawatt 11,200 idan aka kwatanta da karfin samar da wuta da ake da shi na megawatt 15,500 a baya.

A halin da ake ciki, masu ruwa da tsaki a bangaren lantarki na kira ga gwamnati da ta ayyana dokar ta-baci a wannan bangare, wanda duk da zuba jari a baya, har yanzu bai samu gyara ba.

Bugu da kari, duk da biliyoyin Naira da aka zuba a bangaren a cikin shekaru biyar da suka gabata, karfin samar da wutar lantarki da ake da shi ya ragu da kashi 15 cikin 100 zuwa megawatt 6,773.10 a 2025, idan aka kwatanta da megawatt 7,792.51 a 2020.

Adadin wutar da ake bukata a Najeriya

Sakamakon yawan jama’a da ya haura mitane miliyan 242, Najeriya na bukatar tsakanin megawatt 30,000 zuwa 100,000 domin samar da wadatacciyar wutar lantarki a fadin kasa.

Kara karanta wannan

Yaki ya yi zafi, Amurka ta fara neman $200bn don ci gaba da farmakin Iran

Wata takarda da jaridar Punch ta samu ta nuna cewa kudaden da aka ce an zuba a bangaren lantarki ba su yi wani tasiri mai ma’ana ba, domin har yanzu samar da wuta a fadin kasar na da rauni matuka.

Hakan ya sa mutane da dama ke komawa amfani da janareto da sauran hanyoyin samar da wuta domin ci gaba da gudanar da kasuwanci da rayuwa.

Me ya jawo koma baya a harkar lantarki?

Hukumar NISO ta bayyana cewa babban dalilin raguwar samar da wuta shi ne rashin isasshen iskar gas ga kamfanonin samar da lantarki.

Tashoshin wutar lantarki masu amfani da gas, wadanda su ne mafi yawa a Najeriya, na bukatar kusan Miliyan 1,629.75 na cubic feet na gas a kullum domin aiki yadda ya kamata.

Sai dai zuwa ranar 23 ga Fabrairu, 2026, an samu kusan miliyan 692 ne kawai a rana, wanda bai kai kashi 43 cikin 100 na adadin da ake bukata ba.

Wannan gibin kusan miliyan 937 a kullum ya takaita yawan wutar da ake iya samarwa, tare da rage wutar da ake rabawa kamfanonin raba wuta (DisCos).

Majalisa ta nemi a cire tallafin wuta

Kara karanta wannan

Gobara ta tilasta wa jirgin yakin Amurka gudu wa daga yakin Iran

A wani rahoton, kun ji cewa kwamitin kasafin kudi na Majalisar Dattawan Najeriya ya bukaci a cire tallafin wutar lantarki gaba daya a kasar nan.

'Yan kwamitin sun bayyana cewa matakin zai taimaka wajen kara yawan kudaden shiga da rage nauyin da ke kan kasafin kudin gwamnatin tarayya.

A cewar sanatoci, duk da kokarin da ake yi na gyaran bangaren wutar lantarki, tallafin da ake biya na ci gaba da zama babban kalubale ga tattalin arzikin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262