Saudiyya Ta Sanar da Ranar da Musulmi Za Su Fara Azumin Watan Ramadan
- Mahukunta a ƙasar Saudiyya sun sanar da ganin jinjirin watan Ramadan ranar Juma'a, 28 ga watan Fabrairu wanda ya yi daidai da 29 ga watan Sha'aban
- A wata sanarwa da hukumomin Saudiyya suka fitar, an umarci ɗaukacin al'ummar Musulmi su tashi da azumi gobe Asabar, 1 ga watan Maris 2025
- Wannan dai na nufin musulmi mazauna ƙasar Saudiyya za su fara azumin wannan shekara 2025 daga ranar Asabar, tuni ibadu suka kankama
- A halin yanzu dai musulman Najeriya na dakon sanarwar ganin wata ko akasin haka daga fadar sarkin Musulmi da ke Sakkwato
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Riyadh, Saudi Arabia - Ƙasar Saudiyya ta sanar da cewa an ga jinjirin watan Ramadan yau Juma'a, 28 ga watan Fabrairu, 2025 daidai da 29 ga watan Sha'aban, 1446H.
Mahukunta a ƙasar sun bayyana cewa gobe Asabar, 1 ga watan Maris, 2025 zai zama farkon watan Ramadan na bana.

Kara karanta wannan
Ramadan: Tinubu ya tura sako ga Musulmi, ya yi albashir kan farashin abinci da fetur

Asali: Twitter
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da shafin hukumar kula da harkokin masallatai biyu masu alfarma watau Inside The Haramai ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ga watan Ramadan a kasar Saudiyya
Sanarwar ta umarci ɗaukacin al'ummar musulmi mazauna ƙasar Saudiyya su tashi da azumi gobe Asabar, 1 ga watan Maris, 2025 daidai da 1 ga watan Ramadan, 1446H.
"An ga jinjirin watan Ramadan a ƙasar Saudiyya kuma idan Allah ya kai mu gobe Asabar, 1 ga watan Maris, 2025, zai kama farkon azumi watau 1 ga watan Ramadan, 1446H," in ji sanarwar.
Tuni ma'abota shafin X suka fara lale maraba da watan bayan sanarwar da aka fitar.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke dakon sanarwa daga fadar mai alfarma sarkin musulmi kan ganin watan a Najeriya.
An yi hasashen samun hadari a Saudiyya
Kafin wannan sanarwa dai hukumar hasashen yanayi ta ce da yiwuwar a samu hadari da gajimare a wasu sassaj ƙasa mai tsarki a lokacin duba jinjirin watan Ramadan.
Jihohin da hukumar ta yi hasashen za a samun hadari ko gajimare sun hada da Riyadh, Makkah, Madinah, Al-Qassim da yankin gabashin Saudiyya.
Sai dai a yankunan iyakar arewa, Al-Jawf, Hail, Tabuk, Najran da Jazan, ana sa ran sararin samaniya zai kasance garau, wanda hakan zai ba da damar ganin jinjirin wata cikin sauki.
Duk da wannan hasashe dai an samu ganin jinjirin watan a sasssan ƙasar Saudiyya, wanda hakan ya tabbatar da cewa gobe Asabar ta kama 1 ga watan Ramadan.
Yadda ake tantance rahoton ganin wata
A wani rahoton, mun kawo maku cewa ɗaya daga cikin ƴan kwamitin duban wata, Simwal Usman Jibril ya jero hanyoyin da ake bi don tantance bayyanar jinjirin wata a lokacin azumi da sauran lokutan shekara.
Malam Simwal ya ce ana amfani da na’ura wajen tantance sabon wata don bambance shi da sauran abubuwa masu kama da shi a sararin samaniya.
Sai dai duk da haka har yanzu ba a fara amfani da ita kai tsaye wajen duba wata a Najeriya ba, sabanin wasu kasashen duniya kamar Saudiyya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng