Jirgin Sama Ya Gamu da Mummunan Hatsari, Sama da Mutum 160 Sun Rasu
- Wani jirgin sama da ya taso daga birnin Bangkok na ƙasar Thailand ya gamu da mummunan hatsari a lokacin sauka a Koriya ta Kudu
- An ruwaito cewa jirgin na ɗauke da fasinjoji 181 kuma zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutum 179 yayin da ake ci gaba da bincike
- Wasu mazauna kusa da filin jirgin sun bayyana yadda jirgin saman ya sauka daga kan titinsa, ya ci karo da wata katanga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
South Korea - Wani jirgin saman fasinja na kamfanin sufurin Jeju Air dauke da mutane 181 ya tarwatse kuma ya kama wuta da safiyar yau Lahadi a kasar Koriya ta Kudu.
Lamarin ya faru ne a birnin Muan, mai tazarar kilomita 290 daga Seoul, babban birnin kasar.
A rahoton da BBC ta wallafa, ma'aikatar sufuri ta gano jirgin saman kirar Boeing 737-800 ya kai shekaru 15 yana aiki kuma ya taso ne daga birnin Bangkok na ƙasar Thailand.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fasinjojin jirgin sama 167 sun rasu a hatsari
Fasinjoji 179 daha cikin 181 da jirgin ya ɗauko sun rasa rayukansu, mutum biyu ne kaɗai suka tsira kuma dukkansu ma'aikata ne.
Rahotanni sun bayyana cewa jirgin saman ya gamu da wannan hatsari ne a lokacin da zai sauka sakamakon tangarɗar na'urar saukarsa ta gaba.
Hakan ya sa jirgin ya kaucewa titin sauka, ya tafi da gudu ya ci karo da wata katangaar kankare, inda ya tarwatse nan take, rahoton Daily Trust.
A halin yanzu dai jami'ai masu aikin ceto na ci gaba da neman gawarwakin sauran fasinjojin yayin da hayaki mai kauri ya turnuke daga tarkacen jirgin.
Yadda jirgin sama ya gamu da hatsari
Shugaban hukumar kashe gobara ta Muan, Lee Jeong-hyeon, ya ce jirgin ya ruguje gaba daya, wutsiya kawai ta rage a cikin tarkacen jirgin.
Yoo Jae-yong, mai shekaru 41, wanda ke zaune a kusa da filin jirgin sama, ya shaida cewa ya ga tartsatsi a gefen dama jim kadan kafin faruwar hadarin.
Wani mai suna Kim Yong-cheol, mai shekaru 70, ya ce jirgin ya gaza sauka da farko, ya koma ya zagayo, sannan ya sake dawowa domin jaraba sauka.
Yong-Cheol ya ce ya ga "Hayaki ya turnuƙe a sararin sama a bayan na jiyo ƙarar fashewa mai ƙarfi".
Jirgi ya samu tangarɗar sauka a Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa wani jirgin sama da ya samu matsala a lokacin da yake shirin sauka a filin Nnamdi Azikwe da ke birnin tarayya Abuja.
Hankulan fasinjojin da ke cikin jirgin ya yi matuƙar tashi yayin da na'urar saukar jirgin ta samu ƴar tangarɗa.
Asali: Legit.ng