Muhimman Abubuwan da Kamata Ku Sani game da Kasafin Kudin 2025

Muhimman Abubuwan da Kamata Ku Sani game da Kasafin Kudin 2025

Abuja - A yau Laraba, 18 ga watan Disamba, 2024, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kudirin kasafin kuɗin shekarar 2025 a gaban Majalisa.

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Tinubu ya isa harabar majalisar ne da misalin karfe 12:10 na rana tare da sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume.

Bola Tinubu.
Jawabin Bola Ahmed Tinubu a gaban majalisa yayin gabatar da kasafin 2025 Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Sauran ƴan tawagar Bola Tinubu sun haɗa da shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin tarayya, Femi Gbajabiamila, ministan kudi, Wale Edun da sauransu.

Shugaba Tinubu ya wallafa cikakken bayanin da ya yi a majalisa loƙacin gabatar da kasafin kudin a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kasafin kuɗin 2025 dai zai laƙume Naira tiriliyan 47.9, Legit Hausa ta tattaro maku cikakken jawabin Tinubu.

Jawabin Tinubu yayin gabatar da kasafin 2025

Ya ku ƴan uwana ƴan Najeriya,

Kara karanta wannan

ACHR: "Tinubu ya yi wani abin da tsofaffin shugabannin Najeriya suka gagara yi"

1. A ƙoƙarin cika daya daga cikin nauyin da tsarin mulki ya dora mani da kuma yadda na himmatu wajen sake gina Najeriya don tabbatar da ci gaba mai dorewa, a yau ina gabatar da kasafin kudin 2025 ga Majalisar Tarayya ta 10.

2. A wannan rana, gaban wannan Majalisa mai albarka, ina mai gabatar maku da kasafin kudi na 2025 a daidai lokacin da kasarmu ke kan siraɗin kai wa matakin ci gaba.

3. Wannan kasafin kudi na 2025 yana kara tabbatar da tsare-tsarenmu na samar da tsaro, arziki, da fata nagari.

Kasafin da muka yi wa taken, “Kasafin gyaran ƙasa: Samar da tsaro da Arziki,” na nuna kudurinmu na daidaita tattalin arziki, kyautata rayuwa da bunkasa Najeriya.

4. Aikin da muka faro na gyara da sake fasalin tattalin arziki watanni 18 da suka gabata yana nan a kan tafarkin da ya dace. Ba zabi ba ne a wurinmu ya zama wajibi don bai wa Najeriya damar samun daukaka.

Ina godiya ga duk wani dan Najeriya da ya fara wannan tafiya ta gyara da ceto ƙasar nan tare da mu.

5. Duk da wahalhalun da ake ciki na san cewa irin waɗannan gyare-gyaren suna da muhimmanci ga al’ummarmu.

Kara karanta wannan

Kasafin 2025: Bayanai sun fara fitowa, Tinubu ya ware sama da N15bn don sayo motoci

6. Ya zama wajibi mu ɗora daga inda muka karɓa a watanni 18 da suka gabata ta hanyar sake fasalin tattalin arzikinmu.

7. Manufar kasafin 2025 da na gabatar a yau ita ce dawo da kwanciyar hankali, tare da cike gibin tattalin arzikinmu, haɓaka ciniki, saka hannun jari, bunƙasa haƙo mai da gas, farfaɗo da masana'antu da uwa uba inganta tattalin arziki.

8. Mun ƙuduri aniyar cewa za mu kasance a kan tafarkin da zai tabbatar da ƙarfafa tattalin arzikinmu da kyautata rayuwar ‘yan Najeriya.

9. Nasarar da muka samu a kasafin 2024 ne ta kawo mu ga kasafin kudin 2025. Manufofin wannan kasafin sun haɗa da tsaro, buɗe ƙofar inganta tattalin arziki, tallafawa matasanmu, gina ababen more rayuwa, da sake fasalin Najeriya.

Halin da tattalin arzikinmu ke ciki

10. Mai girma shugaban Majalisar dattawa da kakakin Majalisar Wakilai, ina farin cikin sanar da ku cewa tattalin arzikinmu ya nuna alamun farfadowa.

11. Sababbin manufofin da muka bullo da su sun fara haifar da sakamako mai kyau, kuma ‘yan Najeriya za su fara ganin sauyi nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Jerin muhimman ɓangarori 4 da Tinubu ya warewa kaso mafi tsoka a kasafin kudin 2025

12. An yi hasashen cewa ci gaban ɗa za a samu a tattalin arzikin duniya a 2024 zai kai kashi 3.2 cikin 100, amma duk da haka kasarmu ta samu gagarumin ci gaba.

  • Tattalin arzikinmu ya karu da kashi 3.46% a zangon uku na 2024, idan aka kwatanta da kashi 2.54% a zangon uku na shekarar 2023.
  • Ajiyar kudinmu na ketare yanzu ta kai kusan Dala biliyan 42, wanda ke ba da kariya mai ƙarfi daga tasirin tattalin arzikinmu a waje.
  • Karuwar kayayyakin da muke fitarwa zuwa kasashen waje ya sa rarar cinikayya ta haɓaka, yanzu ya kai Naira tiriliyan 5.8, a cewar hukumar ƙididdiga ta ƙasa.

13. Waɗannan sakamakon da ke nuna farfaɗowar tattalin arziki, tare da wasu, sun ƙara bayyana ƙarfin tattalin arzikinmu da tasirin manufofin da muka tsara tun daga farko.

Aiwatar da kasafin kudin 2024

14. Ina farin cikin sanar da wannan Majalisa cewa gwamnatina ta samu manyan nasarori a aiwatar da kasafin kudin 2024.

A shekarar 2024, mun cimma:

  • Mun tara Naira tiriliyan 14.55 a matsayin kudaden shiga, wanda ya kai kashi 75 cikin 100 na hasashenmu a zangon uku na shekarar.
  • Naira tiriliyan 21.60 a matsayin kudaden kashewa na yau da kullum, wanda ya kai kashi 85 cikin 100 na burinmu a zangon uku na shekarar.
  • 15. Duk da ƙalubalen da ake fuskanta, mun inganta tattara kudaden shiga kuma mun cika manyan wajibai. Tasirin wannan ga tattalin arzikinmu ya fara bayyana a hankali.

Kara karanta wannan

Karyar ƴan bindiga da sauran miyagu ta kare a Najeriya, sanata ya hango shirin Tinubu

Manufofin kasafin kudin 2025

16. Manufofin wannan kasafi na shekarar 2025 sun haɗa da:

  • Daidaita tattalin arzikin kasa.
  • Inganta yanayi mai kyau don gudanar da kasuwanci.
  • Samar da ci gaba mai ɗorewa, ayyukan yi da rage talauci.
  • Sake fasalin rabon kudaden shiga cikin adalci da inganta rayuwar mutane.

17. Yadda aka kasafta kudin wannan kasafi ya nuna muhimman abubuwan da gwamnatin nan ta fi ba fifiko, musamman wajen aiwatar da ajendar sabunta fata.

Takaitaccen bayanin kasafin 2025

18. Alƙaluman kasafin 2025 wani babban lamari ne mai ban sha’awa game da yadda za mu sake gina tsarin tattalin arziki da zamantakewar al’umma:

  • A 2025, muna sa ran tara kudin shiga kimanin Naira tiriliyan 34.82.
  • Ana hasashen kuɗin da gwamnati za ta kashe a 2025 zai kai Naira tiriliyan 47.90, ciki har da naira tiriliyan 15.81 da za a biya bashi.
  • Jimillar gibin kasafin kudin zai kasance naira tiriliyan 13.08, wanda yake daidai da kashi 3.89 cikin 100 na ƙarfin tattalin arzikinmu watau GDP.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya tafi hutu bayan gabatar da kasafin kudin 2025

19. Wannan kasafin kudi yana da matukar ƙarfi kuma yana da mahimmanci wajen inganta makomarmu.

20. Kasafin kudin ya yi hasashen cewa hauhawar farashi zai ragu daga kashi 34.6% zuwa kashi 15% a 2025 yayin da darajar Naira za ta ƙaru daga N1,700 zuwa N1,500/1$.

An kuma yi hasashen cewa za a haƙo ɗanyen man fetur har ganga miliyan 2.06 a kowace rana.

21. Waɗannan hasashen sun ta’allaka ne kan abubuwa kamar haka:

  • Rage shigo da man fetur daga ketare sannan kuma za a samu ƙaruwar fitar da tattaccen mai daga Najeriya zuwa ƙasashen ketare.
  • Ƙaruwar samun amfanin gona sakamkon ingantaccen tsaro wanda zai sa a rage shigo da kayam abinci daga waje.
  • Karuwar kudaden waje a kasuwar musayar kudi ta hanyar masu saka hannun jari daga ƙetare.

Muhimman abubuwan da aka warewa kudi mai tsoka

22. Kasafta kuɗaɗe zuwa ɓangarorin da suka dace yana cikin muhimman abubuwan da wannan gwamnati ta fi bai wa fifiko a ajendarta ta sabunta fatan ƴan Najeriya.

23. Muhimman sassan da aka warewa kudi mai tsoka sun hada da:

Kara karanta wannan

Kasafin kudi: Bola Tinubu ya sanya kowace Dala a kan N1500 a shekarar 2025

  • Tsaro: Naira tiriliyan 4.91
  • Kayayyakin more rayuwa: Naira tiriliyan 4.06
  • Lafiya: Naira tiriliyan 2.48
  • Ilimi: Naira tiriliyan 3.52

Bayanin kammalawa

Cikin farin ciki, ina gabatar da kasafin kudin 2025 a wannan zaman haɗin guiwa na Majalisar Tarayya.

Allah ya albarkaci Najeriya!

Bola Ahmed Tinubu, GCFR

Shugaban Kasa, Babban Kwamandan Rundunar Sojojin Najeriya.

Bola Tinubu ya tafi hutu Legas

A wani rahoton, an ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tiinubu ya sauka a filim sauka da tashin jiragen sama da ke Legas bayan gabatar da kasafin 2025.

Tinubu ya tafi Legas ne domin yin hutun Kirsimeti da sabuwar shekara wanda za a yi a karshen watan Disamba da farkon watan Janairu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: