Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Sabon Hafsan Rundunar Sojojin Ƙasar Najeriya

Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Sabon Hafsan Rundunar Sojojin Ƙasar Najeriya

  • Majalisar dattawa ta fara tantance muƙaddashin hafsan rundunar sojojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede a zaman ranar Laraba
  • Wannan na zuwa ne bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci majalisar ta amince naɗin Oluyede a matsayin hafsun sojojin ƙasa
  • Shugaban kwamitin kula da sojojin ƙasa na Najeriya, Sanata Abdul'aziz Yari ya ce za su tantance Oluyede ne domin gane ƙwarewarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Majalisar dattawan Nsjerita ta fara tantance muƙaddashin hafsan sojojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede a wani zama na sirri a Abuja.

Majalisar ta fara tantance shi kamar yadda shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya buƙata domin tabbatar da naɗinsa a matsayin cikakken hafsan sojojin kasa.

Godswill Akpabio da Laftanar Janar Oluyede.
Majalisar dattawa ta fara tantance muƙaddashin hafsan sojojin kasa Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta tattaro cewa majalisar ta fara wannan aiki ne a zamanta na yau Laraba, 27 ga watan Nuwamba, 2024 a Abuja.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu da uwar gidarsa za su lula zuwa ƙasar waje

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar dattawa ta fara tantance Janar Oluyede

Gabanin fara zaman sirri, shugaban kwamitin da ke kula da harkokin sojojin ƙasa, Sanata Abdul'aziz Yar'adua ya tunatar da abokan aikinsa wasiƙar da Tinubu ya aiko.

Ya ce shugaban ƙasa ya bukaci majalisar ta tabbatar da naɗin Oluyede a matsayin sabon hafsan rundunar sojin ƙasa a wasiƙar da ya turo ranar Talata.

Abdul'aziz 'Yar'adua ya yi ta'aziyya ga Oluyede bisa rasuwar magabacinsa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.

Majalisa ta yabawa rundunar sojojin Najeriya

"Kowa ya san yadda kalubalen tsaro ya zame wa kasar nan karfen ƙafa kuma muna bukatar lalubo bakin zaren cikin gaggawa."
"Zan yi amfani da wannan damar wajen yabawa dakarun rundunar sojojin kasa da sauran hukumomin soji bisa nasarar da suka samu da yaƙi da ta'addanci da sauran miyagu a faɗin ƙasar nan."
"Dakarun suna wannan yaƙi da jarumta har wasu daga ciki na rasa rayukansu, sun cancanci a jinjina masu.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun hallaka 'yan ta'addan Boko Haram a wani hari

- Abdul'aziz Yar'adua.

Sanata Abdul'aziz ya ce za a yi wannan tantancewa ne domin tabbatar da gogews da kwarewar Oluyede.

Majalisar wakilai za ta binciki daukar aiki

Rahoto ya gabata cewa 'yan majalisar wakilan tarayya za su gudanar da bincike a kan yadda aka dauki aiki a wasu ma’aikatu.

A lokacin, an ji cewa Hon. Isa Ali ya jawo za a binciki hukumomin FIRS, CAC da kuma NDIC, rahoto zai bayyana cikin makonni hudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262