Ondo 2024: Jam'iyyun Siyasa Sun Ɓullo da Sabuwar Dabarar Sayen Kuri'un Mutane

Ondo 2024: Jam'iyyun Siyasa Sun Ɓullo da Sabuwar Dabarar Sayen Kuri'un Mutane

  • Jam'iyyun siyasa sun bullo da sabuwar dabarar sayen kuri'un mutane a zaben da ke gudana yau Asabar a jihar Ondo
  • An ruwaito cewa wakilan jam'iyyu su na bai wa duk wanda ya zabi ɗan takararsu takarda da nufin za a ba shi kudin bayan zaɓe
  • Masu kaɗa kuri'a a wata rumfar zaɓe sun tabbatar da wannan lamarin, sun ce ba su san adadin kudin da wakilan za su bayar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Yayin da harkokin zabe suka kankama a jihar Ondo yau Asabar, an samu labarin jam'iyyun siyasa sun dage wajen ssyen kuri'un mutane

Rahotanni sun bayyana yadda wakilan jam'iyyu a wasu akwatunan zaɓe suka bullo da sabuwar dabarar sayen kuri'u ta yadda za su kaucewa jami'an tsaro.

Zaben Ondo.
Yadda ake cin kasuwar kuri'u a zaben gwamnan jihar Ondo Hoto: Edo Election
Asali: Facebook

Ondo: Jam'iyyun siyasa sun ɓullo da dabara

Kara karanta wannan

Ondo 2024: Yadda ake cakewa mutane kuɗin Kuri'u a kusa da jami'an EFCC

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa wasu wakilan jam'iyyu suna rabawa mutane takarda mai ɗauke da sa hannu a matsayin shaidar sun zaɓi ɗan takararsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan dai na zuwa ne yayin da zaɓe ya kankama a mafi yawan rumfunan zaɓe yau Asabar 16 ga watan Nuwamba, 2024.

Ma'aikatan wucin gadi na hukumar zaɓe mai zama kanta watau INEC sun isa rumfunan zaɓe a kan lokaci.

Manyan ƴan takara a zaben sun haɗa da Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jam'iyyar APC da Agboola Ajayi na jam'iyyar PDP.

Bayan fara kaɗa kuri'a, jami'an DSS sun yi nasarar cafke wasu masu sayen kuri'u da makudan kudaɗe a tattare da su.

Wakilan jam'iyyu sun koma raba takarda

An ruwaito cewa yanzu kuma wakilan jam'iyyun siyasa sun bullo da dabarar ba mutum takarda mai ɗauke da sa hannu bayan ya zaɓi ɗan takararsu.

Masu kaɗa kuri'a a rumfar zaɓe ta 007 da ke gunduma ta 2 a ƙaramar hukumar sun ce ana ba su takardar ne domin ta zama shaidar da za su karɓi kudi daga wakilan jam'iyyun bayan zaɓe.

Kara karanta wannan

Ondo: An tarwatsa masu zabe da miyagu suka yi ta harbe harbe, an gano dalili

Ɗan takarar LP a zaben Ondo ya kaɗa kuri'a

A wani rahoton, an ji cewa Dan takarar gwamnan jihar Ondo karkashin jam'iyyar LP, Festus Ayo Olorunfemi ya kada kuri’arsa a yau Asabar.

An rahoto cewa Olorunfemi ya kada kuri’ar ne a mazabarsa Ajowa-Akoko, karamar hukumar Akoko ta Arewa maso Yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262