Uwargidar Shugaban Kasa da Wasu Ƙusoshi 2 Sun Dura Gidan Marigayi Hafsan Sojin Ƙasa
- Uwargidar shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu ta kai ziyara gidan marigayi hafsan sojojin ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja
- Oluremi ta yi ta'aziyya ga matar marigayin, Mariya Lagbaja da sauran ƴan uwansa, inda ta buƙaci su zama masu juriya da wannan rashi
- Matar mataimakin shugaban ƙasa, Hajiya Nana Shettima da matar mai ba da shawara kan tsaron ƙasa, Nuhu Ribadu na tare da Sanata Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osun - Uwargidar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayi babban hafsan sojin ƙasa (COAS), Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.
Ta kai wannan ziyara ne tare da matar mataimakin shugaban ƙasa, Hajia Nana Shettima, da matar mai ba da shawara kan tsaron ƙasa, Hajia Ribadu.
Mai ɗakin babban hafsan hafsoshin sojojin ƙasar nan (CDS), Misis Oghogho Musa ce ta tarbi uwargidar shugaban ƙasa da ƴan tawagarta, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matar Tinubu ta yi ta'aziyya ga iyalan Lagbaja
A yayin ziyarar, Sanata Oluremi Tinubu ta yi addu’a da ta’aziyya ga iyalan marigayi Lagbaja bisa wannan babban rashi da suka yi.
Da take rarrashin matar marigayin, Misis Mariya Abiodun Lagbaja da ƴaƴansa, Sanata Oluremi Tinubu ya tuna masu cewa rayuwa da mutuwa suna hannun Allah.
'Rayuwa da mutuwa na hannun Allah'
Uwargidar shugaban ƙasar ta tunatar da su cewa Allah ne kaɗai ya san lokacin da kowane ɗan adam zai mutu, babu wanda ya sani bayan Shi.
A wata sanarwa da mai ba matar shuaban ƙasa shawara kan harkokin midiya, Busola Kukoyi, ta fitar. ta haƙaito Oluremi Tinubu na ƙara ba su hakurin wannan rashi.
Sanata Tinubu ta roki iyalan marigayin da su yi koyi da kyawawan halayen da ya mutu ya bar masu, kamar yadda The Nation ta kawo.
Bugu da ƙari, matar shugaban ƙasan ta kuma ja hankalin yaran da su tsaya tsayin daka kan duk abin da suka sa a gaba kuma su kiyaye kimar mahaifinsu.
Gwamnonin Arewa sun yi ta'aziyya
A wani labarin, an ji cewa gwamnonin jihohin Arewa 19 sun yi wa shugaba Bola Tinubu ta'aziyyar rasuwar hafsan sojojin ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.
Shugaban kungiyar gwamnonin Arewa NSGF kuma gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya ne ya mika sakon ta'aziyyar a wata sanarwa.
Asali: Legit.ng