Gwamma Ya Amince da N77,000 a Matsayin Sabon Mafi Ƙarancin Albashin Ma'aikata

Gwamma Ya Amince da N77,000 a Matsayin Sabon Mafi Ƙarancin Albashin Ma'aikata

  • Gwamna Dapo Abiodun ya amince da N77,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikatan gwamnati a jihar Ogun
  • Bayan ganawa da kungiyoyin ƴan kwadago reshen jihar, Gwamna Abiodun ya sanar da cewa sabon albashin ma'aikatan zai fara aiki nan take
  • Abiodun ya zama gwamna na uku kenan da ya ɗora wani abu a kan N70,000 da aka amince ya zama sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ogun - Gwamna Dapo Abiodun ya bayyana N77,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi a jihar Ogun wanda zai fara aiki nan take.

Gwamnan ya amince da hakan ne bayan ganawar wakilan gwamnatin Ogun karkashin jagorancin sakatare, Mr. Tokunbo Talabi da ƙungiyoyin kwadago a Abeokuta.

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa ya zabtare 55% a farashin shinkafa da wasu kayan abinci

Gwamna Dapo Abiodun.
Gwamnan Ogun ya amince da N77,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi Hoto: @DapoAbiodunCON
Asali: Twitter

Gwamnatin Ogun ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na manhajar X ranar Litinin, 14 ga watan Oktoba, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan kwadago sun jijinawa gwamnan Ogun

Bayan wannan taro, jagororin ƴan kwadago sun yabawa gwamnan bisa amincewa da mafi ƙarancin albashin da ya zarce na sauran jihohi a ƙasar nan.

Shugaban NLC a Ogun, Kwamared Hameed Benco ya ce jihar ta ciri tuta wajen biyan albashi mafi tsoka, inda ya ce sauran jihohi na ba da N77,000 ko ƙasa da haka.

Kazalika shugaban kungiyar TUC da takwaransa na JNC sun jinjinawa gwamnatin Ogun, inda suka ce nan ba da jimawa za a ƙara fansho.

Gwamna Abiodun ya damu da ma'aikata

A nasa jawabin shugaban ma’aikata na jihar Ogun, Kehinde Onasanya, ya yi maraba da sabon albashin, ya ce gwamnan ya damu da walwalar ma’aikata.

Kara karanta wannan

Ana zargin gwamna a Arewa na shirin rusa fadar sarki mai tarihi da Masallacin Juma'a

Abiodun zai zama gwamna na uku a Najeriya da ya ɗora wani abu a kan sabon mafi ƙarancin albashi na ₦70,000 bayan Ahmed Ododo na kogi da Lucky Aiyedatiwa na Ondo.

NLC ta gargaɗi jihohi kan sabon albashi

A wani rahoton kun ji cewa ƙungiyar kwadago ta kara daukar zafi kan maganar karin mafi ƙarancin albashin ma'aikata zuwa N70,000 a Najeriya.

Shugaban kwadago, Joe Ajaero ya ce suna shirye kan ɗaukar mataki a dukkan jihohin Najeriya da suka gaza kara albashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262