Arewa na Cikin Matsala, Ambaliya Ta Kara Kashe Mutum 29, Gidaje 321,000 Sun Lalace

Arewa na Cikin Matsala, Ambaliya Ta Kara Kashe Mutum 29, Gidaje 321,000 Sun Lalace

  • Ambaliyar ruwa ta laƙume rayukan mutum 29 tare da lalata dubban gidaje da gonaki a ƙananan hukumomi 16 a Kebbi
  • Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Yakubu Ahmed ya ce ruwan ya rusa gidaje 321,000 da gonakin mutane 858,000
  • Ya yi kira ga gwamnatin tarayya, ƙungiyoyi da ɗaidaikun mutane su tallafawa jihar domin ta tunkari wannan ibtila'i

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ta bayyana cewa akalla mutane 29 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku a kananan hukumomi 16 cikin 21.

Gwamnatin ta ce bayan asarar rayuka, mutane sun tafka asarar gidaje 321,000 da amfanin gonaki aƙalla 858,000 a ambaliyar ruwan da aka yi.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya fara rabawa waɗanda ambaliya ta shafa kuɗi da kayan abinci

Taswirar jihar Kebbi.
Gwamnatin Kebbi ta bayyana ɓarnar da ambaliya ta yi a kananan hukumomi 16 Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Kwamishinan yaɗa labarai, Yakubu Ahmed ne ya bayyana haka da yake hira da manema labarai a Birnin Kebbi yau Jumu'a, 27 ga watan Satumba, Daily Trust ta kawo labarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ambaliyar ruwan Kebbi ta yi muni

Ya ce idan ba a kai wa waɗanda ibtila'in ya shafa ba, za a iya shiga matsalar ƙarancin abinci a jihar Kebbi da ma Najeriya baki ɗaya.

A cewar Yakubu, manoma sun yi asarar amfanin gonakinsu kamar masara, shinkafa, waken suya da sauran makamantansu, kuma hakan ba karamar illa bace.

Ya ce tun kafin hasashen NiMET na cewa Kebbi na iya fuskantar ambaliya, jihar ta fuskanci bala'i mai tsanani sakamakon mamayar ruwa a kananan hukumomi 16.

Me ya haddasa ambaliya a Kebbi?

A cewarsa, ambaliyar ta afku ne sakamakon ruwan da aka saki daga madatsar Goronyo da ruwan kogin Rima da Kogin Kaa wanda ke kwarara cikin jihar ta kogin Niger.

Kara karanta wannan

Ana raɗe raɗin gwamna na shirin sauya sheƙa, ciyamomi sun fice daga jam'iyyar PDP

A rahoton Vanguard, Yakubu Ahmed ya ce:

"Ƙananan hukumomi biyar daga cikin 16 ne kaɗai za a iya cewa ɓarnar da sauƙi, amma ambaliyar ta lalata filayen gonaki, gadoji da dubban gidaje.
"Dangane da waɗanda suka rasu, mun rasa rayukan mutum bakwai a Shanga, takwas a Maiyama, biyar a Kalgo, bakwai a Jega da mutum biyu a Birnin Kebbi.

Kwamishinan ya yi kira ga gwamnatin tarayya, kungiyoyi masu zaman kansu da sauran masu hannu a shuni su tallafawa jihar domin ragewa waɗanda lamarin ya shafa raɗaɗi.

Ambaliya ta yi ɓarna a Kebbi da Neja

Rahotanni sun nuna ambaliyar ruwa ta yi kaca-kaca da amfanin gonakin al'umma a wasu yankuna da ke jihohin Kebbi da Neja.

Hukumar N-HYPPADEC ta miƙa sakon jaje ga waɗanda ibtila'in ya shafa tare da yabawa matakin gwamnatin tarayya na ware N3bn.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: