Wasu Dattawa Sun Sake Taɓo Batun Ƙisan Sarkin Gobir, Sun Roki Alfarmar Tinubu da Gwamna
- Dattawan Gobir sun roki gwamnatin tarayya da ta jihar Sakkwato su ba da umarnin a kwato gawar Sarkin Gobir domin a masa jana'iza
- Kungiyar bunƙasa yankin Gobir (GDA) ce ta bayyana hakan ranar Litinin ta bakin mai magana da yawunta Farfesa Iliyasu Yusuf Gobir
- Marigayi Sarkin Gobir, Alhaji Muhammad Isa Bawa ya rasa ransa ne bayan ƴan bindiga sun yi garkuwa da shi a watan Agusta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Sokoto - Ƙungiyar bunƙasa yankin Gobir (GDA) wacce ta wakilci dattawan yankin ta sake taɓo batun kisan sarkin Gobir, Isah Muhammad Bawa.
Ƙungiyar ta roki gwamnatin Bola Tinubu da Gwamna Ahmed Aliyu na Sakkwato su taimaka su sa a tono gawar Sarkin Gobir domin yi masa jana'iza mai kyau.
Mai magana da yawun kungiyar GDA, Farfesa Iliyasu Yusuf Gobir, shi ne ya nemi wannan alfarmar a wata hira da ƴan jarida ranar Litinin a Kano, Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴan bindiga suka kashe Sarkin Gobir
Wasu ‘yan bindiga sun kashe Sarkin Gobir kuma Hakimin Gatawa, Alhaji Isa Muhammad Bawa a lokacin da suka yi garkuwa da shi a ranar 21 ga Agusta, 2024.
‘Yan bindiga sun sace shi a ranar 27 ga Yuli, 2024 tare da dansa Kabiru Isa a lokacin da suke dawowa daga wani taro a fadar Sarkin Musulmi da ke Sakkwato.
Kakakin GDA Farfesa Iliyasu Yusuf Gobir, ya bayyana takaicinsa kan rashin tsaro da ake fama da shi da kuma yadda gwamnati ke nuna halin ko in kula, rahoton Leadership.
Meyasa suke neman a ɗauko gawar sarkin?
Ya kuma jaddada bukatar gwamnati ta dauki matakin gaggawa na zuwa daji a tono gawar marigayi Sarkin da kuma magance matsalolin tsaron da al’ummar Gobir ke fuskanta.
"Al’ummar Hausawa musamman na Gobir sun nuna hakuri da juriya a halin rashin tsaron da ake fama da shi, amma duk da haka haƙurin mu na neman karewa."
"Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Sokoto su dauki kwaƙkwaran mataki domin kawo karshen kashe-kashe da sace-sacen mutane."
“Masarautar Gobir tana bukatar gwamnatin tarayya da ta Sakkwato su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an dawo da gawar Sarkin Gobir domin al’ummarsa su yi masa jana’iza mai daraja.
- Farfesa Iliyasu Gobir.
An kama ƴan leken asirin ƴan bindiga
A wani rahoton kuma Gwamna Dikko Radda ya ce dakarun rundunar tsaron da ya ƙirƙiro sun kama ƴan leƙen asiri akalla 1000 masu taimakawa ƴan bindiga a Katsina
Malam Dikko Raɗda ya ce gwanatinsa ta gano tushen matsalar tsaron jihar kuma ta maida hankali wajen magance su
Asali: Legit.ng