DHQ: Ƴan Ta'adda Sama da 120,000 Sun Ajiye Makamai, Sun Miƙa Wuya ga Sojojin Najeriya

DHQ: Ƴan Ta'adda Sama da 120,000 Sun Ajiye Makamai, Sun Miƙa Wuya ga Sojojin Najeriya

  • Hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta bayyana cewa zuwa yanzu ƴan ta'adda akalla 125,517 sun miƙa wuya ga dakarun sojoji
  • Shugaban sashen ayyuka na DHQ, Manjo Janar Emeka Onumajuru ya ce sojoji sun samu nasarar magance ayyukan ƴan ta'adda
  • Ya ce rundunar soji da haɗin guiwar gwamnatin Borno sun maida ƴan gudun hijira da dama zuwa gidajensu a Arewa maso Gabas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Shugaban sashen bada horo da ayyuka a hedikwatar tsaro, Manjo Janar Emeka Onumajuru, ya ce kawo yanzu ‘yan ta’adda 125, 517 da iyalansu sun mika wuya ga sojoji.

Ya faɗi haka ne a wurin wani taron manema labarai da babban hafsan tsaron, Janar Christopher Musa ya jagoranta a Abuja ranar Talata.

Kara karanta wannan

Borno: Mutanen Maiduguri sun wayi gari da labari mai daɗi bayan ambaliyar da ta afku

Janar Christopher Musa.
Hedikwatar tsaro DHQ ta bayyana cewa ƴan ta'adda 125,517 sun miƙa wuya ga sojoji Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

Borno: An fara maida ƴan gudun hijira gida

Onumajuru ya bayyana cewa rundunar sojoji da haɗin guiwar gwamnatin jihar Borno sun mayar da wasu ƴan gudun hijira zuwa gidajensu, Daily Trust ta rahoto.

"Sojoji da haɗin guiwar gwamnatin Borno sun mayar da ƴan gudun hijira sama da 60,000 zuwa gidanjensu, wanda hakan ya rage cunkoso a sasanonin ƴan gudun hijira," in ji shi.

Manjo Onumajuru ya shaida wa manema labarai cewa a halin yanzu jami'an tsaro sun shawo kan matsalar tsaro a Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Gabas. 

A cewarsa, sojoji sun shafe batun dokar zaman gida ta ranar Litinin da kungiyar ƴan aware IPOB ta ƙaƙabawa mutane a Kudu maso Gabas.

Sojoji sun muƙushe mayaƙan IPOB

Bugu da ƙari, babban jami'in sojin ya ce dakaru sun yi nasarar kawar da mayaƙan haramtacciyar kungiyar IPOB da dama.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya bayyana adadin mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Borno

A ruwayar Leadership, Onumajuru ya ce:

"Mun shawo kan rikicin jihar Filato ta hanyar ayyukan sojoji na kwantar da tarzoma. Haka nan sojojin da aka tura Banyo a jihar Nasarawa sun magance hare-haren ƴan bindiga."

Sojoji sun kashe ƴan bindiga 8 a Kaduna

A wani rahoton kuma gwarazan sojojin Najeriya sun hallaka ƴan bindigar daji takwas a yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Gwamnatin Kaduna ta ce sojojin sun sheƙe ƴan ta'addar ne a lokacin da suka fita sintiri a kewayen Kamfanin Doka da Gayam.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262