Ambaliya: Gwamna Zulum Ya Yi Bayanin Halin da Ake Ciki, Ya Faɗi Kuɗin da Tinubu Ya Turo

Ambaliya: Gwamna Zulum Ya Yi Bayanin Halin da Ake Ciki, Ya Faɗi Kuɗin da Tinubu Ya Turo

  • Gwamna Babagana Zulum ya yi bayanin halin da ake ciki game da ambaliyar ruwan da ta afku a Maiduguri da wasu yankuna a Borno
  • Zulum ya fara rabawa mutanen da suka rasa matsugunansu kayan agaji da tsabar kudi, ya ba da kwangilar dafa masu abinci
  • Gwamnan ya kuma tabbatar da jihar Borno ta karɓi tallafin N3bn daga gwamnatin tarayya domin magance wasu matsalolin da aka shiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno - Sama da mutane miliyan daya ne suka rasa matsugunansu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umaru Zulum ne ya tabbatar da hakan a ranar Laraba, 11 ga watan Satumba, 2024.

Kara karanta wannan

Borno: Mutanen Maiduguri sun wayi gari da labari mai daɗi bayan ambaliyar da ta afku

Gwamna Babagana Umaru Zuum.
Gwamna Zulum ya fara rabawa mutanen da ambaliya ta raba da mahallansu kayan agaji da kuɗi Hoto: Professor Babagana Umara Zulum
Asali: Facebook

Channels tv ta ce Zulum ya raba tsabar kudi ga mutanen da ke mafaka a sansanin ‘yan gudun hijira na Bakassi da ke kan hanyar Biu-Damboa a Maiduguri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zulum ya karɓi tallafin N3bn daga Gwamnatin Tinubu

Zulum ya ce wannan somin tabi ne domin za a rabawa mutane abinci da kayan masarufi, kuma a cewarsa tuni ya ba masu abinci kwangilar ciyar da mutanen da suka rasa matsugunansu.

Farfesa Zulum ya tabbatar da cewa Borno ta samu tallafin N3bn daga gwamnatin tarayya kuma za a yi amfani da kuɗin wajen magance ƙalubalen ambaliyar ruwa.

Gwamnatin Zulum za ta kafa kwamiti

Gwamna Zulum ya ce domin daƙile abin da ka iya zuwa ya dawo, gwamnan ya ce za a kafa kwamitin lafiya da zai duba yiwuwar ɓarkewar cututtukan bayan abin da ya faru.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya bayyana adadin mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Borno

Ya ce tuni jami'an hukumomin agaji suka fara aikin ceto a duka yankunan da ibtila'in ya shafa domin tantance rayukan da aka rasa da waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Menene ya jawo ambaliya a Maiduguri?

Dangane da musabbabin ambaliyar, Gwamna Zulum ya ce ruwan sama mai yawa da aka samu a bana ne ya kawo wannan ambaliya, Daily Trust ta rahoto.

Zulum ya ce ambaliyar ta afku ne sakamakon kwararar ruwa daga Alau dam, wanda ya cika maƙil sakamakon sakin ruwa daga madatsun ruwa na Kamaru.

Gwamnan ya ce za a sake gina Alau Dam domin ƙara masa faɗin da zai ɗauki adadi mai yawa na ruwa, sannan gwamnati za ta rushe gine-ginen da aka yi a hanyar ruwa.

Borno: Jami'an SEMA sun maƙale

A wani rahoton kuma jami'an hukumar ba da agajin gaggawa ta Borno SEMA sun maƙale a wani yanki da suka je kai kayan agaji da ceto mutane.

Kara karanta wannan

Manyan abubuwa da aka wayi gari da su a Maiduguri bayan ambaliya

Shugaban SEMA, Barkindo Mohammed na cikin tawagar jami'an da suka maƙale bayan kai wa mutane ɗauki a yankin Gozari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: