A Ƙarshe Shugaba Tinubu Ya Faɗi Ayyukan da Yake Yi da Kudin Tallafin Man Fetur

A Ƙarshe Shugaba Tinubu Ya Faɗi Ayyukan da Yake Yi da Kudin Tallafin Man Fetur

  • Bola Ahmed Tinubu ya yi ƙarin haske kan babban dalilinsa na cire tallafin man fetur duk da wahalar da ake sha a Najeriya
  • Shugaban ƙasar ya ce ya tuge tallafi ne domin tara kuɗaɗen da za a samar da ababen more rayuwa da inganta walwalar al'umma
  • Ya buƙaci 'yan kasuwa da sauran al'umma su ba gwamnati haɗin kai a kokarin da take yi na dawo da tattalin arziki kan turba mai kyau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa ta cire tallafin man fetur ne saboda a samu isassun kuɗaden shiga da za a yi wa ƴan Najeriya aiki.

Shugaba Tinubu ya ce ba domin ƙuntatawa mutane ya ɗauki wasu matakai ba, ya yi haka ne domin ceto tattalin atzikin ƙasar nan wanda ya fara tangal-tangal.

Kara karanta wannan

"Har da kai a ciki": APC ta caccaki tsohon jigonta kan sukar Buhari da Tinubu

Shugaba Bola Tinubu.
Bola Tinubu ya ce ya cire tallafinan fetur ne domin farfaɗo da tattalin arziƙi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shugaban ƙasar ya faɗi haka ne a ranar Talata yayin da ya bude taron shekara-shekara na CIBN karo na 17 wanda aka gudanar a Abuja, Daily Trust ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima shi ne ya wakilci Bola Tinibu a wurin taron mai taken, "bunƙasa tattalin arziki da ci gaban ƙasa,"

Wane kokarin Bola Tinubu ke yi?

Da yake bayyana kokarin da gwamnatinsa ke yi na farfaɗo da tattalin arzikin kasar, Shugaba Tinubu ya ce:

"Mun taka matakai masu tsauri domin farfaɗo da tattalin arzikinmu, manufarmu ita ce ceto tattalin arziƙi ta hanyar rage hauhawar farashin kayayyaki, daidaita farashin canji da gyara kasafi."
"Duk da akwai raɗaɗi a farko amma mun tuge tallafin mai ne domin amfani da kuɗaɗen wajen gina ababen more rayuwa da walwalar al'umma."

Wane ɓangare Tinubu ya tura kudin tallafi?

Kara karanta wannan

Malami ya gayawa Tinubu kuskuren da yake yi kan tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya

Shugaba Tinubu ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen samar da ababen more rayuwa a yunkurinta na bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Ya buƙaci haɗin kan kowane ɓangaren kama daga gwamnati, ƴan kasuwa da kamfanoni masu zaman kansu da sauran al'umma domin cimma nasara, inji The Cable.

Zuwan shugaba Tinubu China ta yi riba

A wani rahoton kuma kun ji cewa ziyarar da shugaban kasa Bola Tinubu ya kai kasar Sin ta yi riba bayan da kasashen biyu suka kulla yarjejeniyar dala biliyan 3.3

An rahoto cewa Najeriya da kasar Sin sun rattaba hannu kan yarjejeniyar bunkasa masana'antar karfen Brass da Methanol da ke Bayelsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: